Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 71

Jehobah Ya Kāre Yesu

Jehobah Ya Kāre Yesu

Akwai wasu mutanen da ke zama a gabas kusa da Isra’ila. Mutanen sun gaskata cewa taurari za su iya yi musu ja-goranci. Wata rana da daddare, sai wasu mutane daga Gabas suka ga wani abu da ya yi kama da tauraro mai haske a sama kuma suka soma bin sa. Wannan “tauraron” ya kai su Urushalima. Sai suka soma tambayar mutane cewa: ‘Ina yaron da zai zama sarkin Yahudawa? Mun zo don mu yi masa sujada.’

Sarkin Urushalima mai suna Hiridus ya ji game da sabon sarkin kuma hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Sai ya tambayi manyan firistoci cewa: ‘A ina ne za a haifi wannan sarkin?’ Sai suka ce masa: ‘Annabawa sun ce za a haife shi a Bai’talami.’ Hiridus ya kira mazan da suka zo daga Gabas kuma ya gaya musu: ‘Ku je Bai’talami ku nemi wannan yaron. Ku dawo kuma ku gaya mini inda yake. Ina so in yi masa sujada.’ Amma abin da ya ce ba gaskiya ba ne.

Sai “tauraron” ya soma tafiya. Mazan sun bi shi har zuwa Bai’talami. “Tauraron” ya tsaya a saman wani gida. Sai mazan suka shiga cikin gidan. Sun ga Yesu da kuma mahaifiyarsa Maryamu. Suka yi wa yaron sujada kuma suka ba shi kyautar zinariya da māi da kuma turare masu tsada. Jehobah ne ya turo waɗannan mutanen wurin Yesu? A’a.

A wannan daren, Jehobah ya gaya wa Yusufu a mafarki cewa: ‘Hiridus yana so ya kashe Yesu. Ka ɗauki matarka da yaron kuma ku gudu zuwa Masar. Ka zauna a wajen har sai na gaya maka cewa ka koma.’ Nan da nan, sai Yusufu da iyalinsa suka tafi ƙasar Masar.

Jehobah ya gaya wa mazan da suka zo daga Gabas cewa kada su koma wurin Hiridus. Hiridus ya yi fushi sosai da ya ga cewa mutanen ba su koma wurinsa ba. Tun da bai san inda zai ga Yesu ba, sai ya ba da umurni cewa a kashe duka yara maza a Bai’talami da shekarunsu ɗaya ne da na Yesu. Amma a lokacin, an riga an kai Yesu Masar.

Da shigewar lokaci, Hiridus ya mutu. Sai Jehobah ya gaya wa Yusufu cewa: ‘Yanzu za ka iya komawa.’ Yusufu da Maryamu da kuma Yesu suka koma Isra’ila kuma suka nemi gida a birnin Nazarat.

“Haka nan kuma maganata, wadda take fitowa daga cikin bakina za ta zama . . . , za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.”​—Ishaya 55:11