Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 90

Yesu Ya Mutu a Golgota

Yesu Ya Mutu a Golgota

Manyan firistoci sun kai Yesu wurin gwamna mai suna Bilatus. Sai Bilatus ya tambaye su: ‘Mene ne kuke zargin sa da shi?’ Suka ce: ‘Ya ce shi Sarki ne!’ Bilatus ya tambayi Yesu: “Kai Sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.”

Sa’an nan Bilatus ya tura shi wurin Hiridus wanda shi ne mai mulkin Galili don ya bincike shi ko yana da laifi. Hiridus bai same shi da laifi ba, sai ya sake tura shi wurin Bilatus. Sai Bilatus ya ce wa mutanen: ‘Ni da Hiridus ba mu sami mutumin nan da laifi ba. Don haka, zan sake shi.’ Mutanen suka yi ihu suna cewa: ‘A kashe shi! A kashe shi!’ Sojojin suka yi wa Yesu bulala, suka tofa masa yau kuma suka buge shi. Sun saka masa rawanin kaya kuma suna cewa: ‘Barka dai Sarkin Yahudawa.’ Bilatus ya sake ce wa mutanen: ‘Ban sami mutumin nan da laifi ba.’ Suka yi ihu suna cewa: ‘A rataye shi a kan gungume!’ Sai Bilatus ya ba da shi don a kashe shi.

Sojojin sun kai Yesu wani wuri da ake kira Golgota, suka kafa masa ƙusa a kan gungume, sai suka ɗaga gungumen sama. Yesu ya yi addu’a ya ce: ‘Ya Uba, ka gafarce su don ba su san abin da suke yi ba.’ Mutanen sun yi ma Yesu dariya, suna cewa: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, ka sauko daga kan gungumen! Ka ceci kanka.’

Ɗaya daga cikin ɓarayin da ke gefensa ya ce: “Ka tuna da ni lokacin da ka soma Mulkinka.” Yesu ya yi masa alkawari cewa: ‘Za ka kasance tare da ni cikin Aljanna.’ Da rana, sai gari ya yi duhu har sa’o’i uku. Wasu daga cikin mabiyan Yesu sun tsaya kusa da gungumen, har da Maryamu mahaifiyar Yesu. Yesu ya ce wa Yohanna ya kula da Maryamu kamar yadda yake kula da mamarsa.

Sai Yesu ya ce: “Ya cika!” Ya sunkuyar da kansa kuma ya ja numfashi na ƙarshe. Nan take, sai aka yi girgizar ƙasa. A cikin  haikali kuma babban labule da ya raba wuri mai tsarki da mafi tsarki ya tsage. Wani soja ya ce: ‘Hakika, wannan Ɗan Allah ne.’

“Gama ta wurinsa ne Allah ya cika dukan alkawuran da ya yi.”​—2 Korintiyawa 1:​20, Juyi Mai Fitar da Ma’ana