Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 9

Gabatarwar Sashe na 9

Wannan sashen ya koya mana game da matasa da annabawa da kuma sarakuna da yawa da suka kasance da bangaskiya. A ƙasar Suriya, wata yarinya ’yar Isra’ila ta yi imani cewa annabin Jehobah zai iya warƙar da Na’aman. Annabi Iliya ya kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah zai kāre shi daga maƙiyansa. Babban Firist mai suna Jehoiada ya sa ransa cikin hadari don ya kāre Jehoash daga hannun kakarsa Athaliah. Sarki Hezekiya ya dogara ga Jehobah don ya san cewa zai ceci Urushalima kuma bai miƙa wuya ga Assuriyawa ba. Sarki Josiah ya cire gumakan da ke ƙasar, ya gyara haikalin Jehobah kuma ya sa mutanensa su soma bauta wa Jehobah.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 51

Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya

Wata karamar yarinya yar Isra’ila ta gaya wa uwar gidanta game da ikon Jehobah kuma hakan ya sa abin al’ajabi ya faru.

DARASI NA 52

Dawaki da Karusan Wuta na Jehobah

yadda aka nuna wa bawan Elisha cewa ‘wadanda suke tare da mu sun fi nasu.’

DARASI NA 53

Jehoiada Ya Yi Karfin Hali

Wani firist mai aminci ya yaki wata muguwar sarauniya.

DARASI NA 54

Jehobah Ya Yi Hakuri da Yunana

Ta yaya babban kifi ya hadiye wani annabin Allah? Ta yaya ya fito daga cikin kifin? Kuma wane darasi ne Jehobah ya koya masa?

DARASI NA 55

Mala’ikan Jehobah Ya Kāre Hezekiya

Makiyan Yahudawa sun ce Jehobah ba zai kāre mutanensa ba amma hakan ba gaskiya ba ne!

DARASI NA 56

Josiah Yana Son Dokar Allah

Josiah ya zama sarki sa’ad da yake dan shekara takwas kuma ya taimaka wa mutanensa su soma bauta wa Jehobah.