Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 97

Karniliyus Ya Sami Ruhu Mai Tsarki

Karniliyus Ya Sami Ruhu Mai Tsarki

Da akwai wani mutum a Kaisariya mai suna Karniliyus. Shi sojan Roma ne. Shi ba Bayahude ba ne amma Yahudawa suna daraja shi sosai. Yana taimaka wa talakawa. Karniliyus ya yi imani da Jehobah kuma yana addu’a a kai a kai. Wata rana, wani mala’ika ya zo wajen Karniliyus kuma ya ce masa: ‘Allah ya ji addu’arka. Yanzu ka tura mutane wurin Bitrus a birnin Yafa kuma ka ce masa ya zo wurinka.’ Nan da nan, sai Karniliyus ya aika maza uku zuwa birnin Yafa. Birnin yana ta kudu kuma yana da nisan wajen mil 30.

Sa’ad da Bitrus yake birnin Yafa, an saukar masa da wahayi. A cikin wahayin, ya ga namomin da aka ce kada Yahudawa su ci. Sai ya ji wata murya tana gaya masa cewa ya ci naman. Bitrus ya ƙi kuma ya ce: ‘Ban taɓa cin nama marar tsabta ba.’ Sai muryar ta ce masa: ‘Kada ka kira waɗannan namomin marar tsarki. Domin Allah ya riga ya tsarkake su.’ Sai aka sake ce wa Bitrus: ‘Akwai wasu maza guda uku a bakin ƙofa, ka bi su.’ Bitrus ya buɗe ƙofar kuma ya tambayi mutanen abin da ya kawo su. Sai suka ce: ‘Karniliyus, wani sojan Roma ne ya aiko mu. Ya ce ka zo gidansa a Kaisariya.’ Bitrus ya gaya wa baƙin cewa su kwana a gidansa. Washegari, sai  shi da wasu ’yan’uwa a birnin Yafa suka bi su zuwa Kaisariya.

Da Karniliyus ya ga Bitrus, sai ya durƙusa a ƙasa. Bitrus ya ce masa: ‘Ka tashi! Ni ma mutum ne kamar kai. Allah ya gaya mini in zo gidanka, duk da cewa bai kamata Yahudawa su shiga gidajen mutanen da ba Yahudawa ba. Ka gaya mini dalilin da ya sa ka ce in zo.’

Sai Karniliyus ya ce wa Bitrus: ‘Kwanaki huɗu da suka shige, sa’ad da nake addu’a ga Allah, sai wani mala’ika ya ce in kira ka. Don Allah ka koya mana game da Jehobah.’ Sai Bitrus ya ce: ‘Yanzu na koyi cewa Allah ba ya nuna wariya. Yana amincewa da duk wanda yake so ya bauta masa.’ Bitrus ya koya musu abubuwa da yawa game da Yesu. Sai ruhu mai tsarki ya sauka a kan Karniliyus da mutanen da ke tare da shi kuma aka yi musu baftisma.

“A cikin kowace al’umma, wanda yake tsoron [Allah], yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.”​—Ayyukan Manzanni 10:35