Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 102

Wahayin da Aka Saukar wa Yohanna

Wahayin da Aka Saukar wa Yohanna

Sa’ad da manzo Yohanna yake kurkuku a tsibirin Batmusa, Yesu ya nuna masa wahayoyi guda 16 da suka nuna abubuwan da za su faru a nan gaba. Waɗannan wahayoyin sun faɗi yadda za a tsarkake sunan Jehobah da yadda Mulkinsa zai zo. Sun kuma nuna yadda za a yi nufinsa a duniya kamar yadda ake yi a cikin sama.

A ɗaya daga cikin wahayoyin, Yohanna ya ga Jehobah a kan kursiyinsa a sama. Ya ga dattawa guda 24 sun kewaye shi kuma suna sanye da fararen kaya da rawanin gwal. Ya ga walƙiya kuma ya ji ƙarar tsawa daga kursiyin. Dattawan guda 24 sun rusuna a gaban Jehobah suna bauta masa. A wani wahayin kuma, Yohanna ya ga mutane da yawa daga dukan al’ummai da ƙasashe da kuma yaruka da suke bauta wa Jehobah. Ɗan ragon, wato Yesu ne yake musu ja-goranci zuwa wajen da akwai ruwan da ke ba da rai. A wani wahayi dabam, ya ga Yesu da kuma dattawan guda 24 sun soma sarauta a sama. A wani wahayi, Yohanna ya ga Yesu yana yaƙi da Shaiɗan da aljanunsa. Yesu ya jefar da su daga sama zuwa duniya.

 Sai Yohanna ya ga wani hoto mai kyau na Ɗan ragon da kuma mutane 144,000 suna tsaye a Dutsen Sihiyona. Ya kuma ga wani mala’ika yana firiya a duniya, yana gaya wa mutane su ji tsoron Allah kuma su bauta masa.

A wani wahayi, ya ga an yi yaƙin da ake kira Armageddon kuma Yesu da rundunarsa sun halaka duniyar Shaiɗan. A wahayi na ƙarshe, Yohanna ya ga kowa a sama da duniya suna da haɗin kai sosai. Ƙari ga haka, an halaka Shaiɗan da masu goyon bayansa gabaki ɗaya. Kowa a sama da duniya suna tsarkake sunan Jehobah kuma suna bauta masa shi kaɗai.

“Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma. Shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.”​—Farawa 3:15