Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 55

Mala’ikan Jehobah Ya Kāre Hezekiya

Mala’ikan Jehobah Ya Kāre Hezekiya

Ƙabilai goma na Isra’ila sun faɗa cikin hannun Assuriyawa. Yanzu kuma sarkin Assuriya mai suna Sennakerib yana so ya mulki ƙabilu biyu na Yahuda. Sai ya soma kwatar biranen da ke Yahuda ɗaya bayan ɗaya. Amma birnin Urushalima ne ya fi so. Sennakerib bai san cewa Jehobah yana kāre Urushalima ba.

Sarkin Yahuda mai suna Hezekiya ya ba Sennakerib kuɗi masu yawa sosai don ya ƙyale Urushalima. Amma Sennakerib ya aika sojojinsa su kai wa Urushalima hari duk da cewa ya karɓi kuɗin. Da Assuriyawan suke gab da kai wa Urushalima hari, sai mutanen suka soma tsoro. Hezekiya ya gaya musu cewa: ‘Kada ku ji tsoro. Ko da yake Assuriyawa suna da ƙarfi, Jehobah zai ba mu ƙarfin da ya fi nasu.’

Sennakerib ya tura bawansa Rabshakeh zuwa Urushalima don ya yi wa mutanen ba’a. Rabshakeh ya tsaya a waje kuma ya yi ihu cewa: ‘Jehobah ba zai taimake ku ba. Kada ku saurari Hezekiya. Babu wani allahn da zai iya kāre ku daga hannunmu.’

Hezekiya ya roƙi Jehobah ya gaya masa abin da ya kamata ya yi. Sai Jehobah ya ce masa: ‘Kada ka ji tsoron abin da Rabshakeh ya ce. Sennakerib bai zai yi nasara a kan Urushalima ba.’ Bayan haka, sai Sennakerib ya rubuta wa Hezekiya wasiƙa. Wasiƙar ta ce: ‘Ka manta kawai. Jehobah ba zai cece ka ba.’ Hezekiya ya sake yin addu’a yana cewa: ‘Ina roƙon ka Jehobah, ka cece mu don dukan mutane su san cewa kai kaɗai ne Allah na gaskiya.’ Sai Jehobah ya gaya masa cewa: ‘Sarkin Assuriya ba zai shiga cikin Urushalima ba. Zan kāre mutanena.’

Sennakerib yana ganin cewa zai yi nasara a kan Urushalima. Amma a daren, sai Jehobah ya aika  mala’ikansa zuwa wajen da sojojin suke. Mala’ikan ya kashe sojoji 185,000! Sarki Sennakerib ya rasa sojojinsa kuma hakan ya sa ya koma gida. Kamar yadda Jehobah ya yi alkawari, ya ceci Hezekiya da kuma Urushalima. Da a ce kana Urushalima a lokacin, shin za ka dogara ga Jehobah?

‘Mala’ikan [Jehobah] yana tsaron waɗanda ke tsoron Ubangiji, ya cece su daga hatsari.’​—Zabura 34:​7, Littafi Mai Tsarki