Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 12

Gabatarwar Sashe na 12

Yesu ya koyar da mutane game da Mulkin Allah. Ya kuma koyar da su cewa su yi addu’a a tsarkake sunan Allah, Mulkinsa ya zo kuma a yi nufinsa a duniya. Idan kana da yara, ka bayyana musu abin da addu’ar nan take nufi. Yesu bai bar Shaiɗan ya hana shi kasancewa da aminci ba. Yesu ya zaɓi manzanninsa kuma suka zama mutanen da aka fara zaɓa don su yi sarauta da shi a sama. Ka lura da himmar da Yesu ya nuna don bauta ta gaskiya. Yana so ya taimaka wa mutane shi ya sa ya warkar da marasa lafiya, ya ta da matattu da kuma ciyar da mayunwata. Mu’ujizojin da Yesu ya yi sun nuna abin da Mulkin Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 74

Yesu Ya Zama Almasihu

Me ya sa Yohanna ya ce Yesu shi ne Dan Rago na Allah?

DARASI NA 75

Shaidan Ya Jarraba Yesu

Shaidan ya jarraba Yesu sau uku. Wadanne abubuwa uku ne ya yi amfani da su don ya jarraba shi? Mene ne Yesu ya yi?

DARASI NA 76

Yesu Ya Tsabtacce Haikalin

Me ya sa Yesu ya dauki bulala kuma ya kori dabbobin da ke haikalin da kuma ture teburan masu canjin kudi?

DARASI NA 77

Yesu da Wata Mata a Bakin Rijiya

Basamariyar da ke kusa da rijiyar Yakubu ta yi mamaki sa’ad da Yesu ya yi mata magana. Me ya sa? Mene ne Yesu ya gaya mata da bai taba gaya wa kowa ba?

DARASI NA 78

Yesu Ya Yi Wa’azi Game da Mulkin Allah

Yesu ya gaya wa wasu mabiyansa su zama masu kama mutane. Bayan wasu lokaci, ya horar da mabiyansa guda 70 don su yi wa’azi.

DARASI NA 79

Yesu Ya Yi Mu’ujizai da Yawa

Duk inda Yesu ya je, marasa lafiya suna zuwa wurinsa don ya taimaka musu kuma ya warkar da su. Har ma ya ta da wata yarinya daga mutuwa.

DARASI NA 80

Yesu Ya Zabi Manzanni Goma Sha Biyu

Me ya sa ya zabe su? Ka san sunansu?

DARASI NA 81

Koyarwa a Kan Dutse

Yesu yana koyar wa taron jama’a wasu muhimman darussa.

DARASI NA 82

Yesu Ya Koya wa Almajiransa Yin Addu’a

Mene ne Yesu ya gaya wa mabiyansa su rika addu’a kai?

DARASI NA 83

Yesu Ya Ciyar da Dubban Mutane

Mene ne mu’ujizar da Yesu ya yi ya koya mana game da Yesu da kuma Jehobah?

DARASI NA 84

Yesu Ya Yi Tafiya a Kan Teku

Ka yi tunanin yadda manzannin suka ji sa’ad da suka ga wannan mu’ujiza

DARASI NA 85

Yesu Ya Yi Warkarwa a Ranar Assabaci

Me ya sa mutane ba sa son abin da yake yi?

DARASI NA 86

Yesu Ya Tayar da Li’azaru Daga Matattu

Da Yesu ya ga Maryamu tana kuka, sai shi ma ya soma kuka. Amma daga bayan, sun daina kuka kuma suka soma farin ciki.