Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 13

Gabatarwar Sashe na 13

Yesu ya zo duniya don ya mutu a madadin ’yan Adam. Duk da cewa ya mutu, ya yi nasara da duniya. Jehobah ya cika alkawarinsa kuma ya ta da Ɗansa daga matattu. Har Yesu ya mutu, ya taimaka wa mutane kuma ya gafarta musu sa’ad da suka yi kuskure. Ya bayyana ga mabiyansa bayan ya tashi daga mutuwa. Ya koya musu yadda za su yi aiki mai muhimmancin da ya ba su. Idan ku iyaye ne, ku taimaka wa yaranku su san cewa mu ma muna sa hannu a wannan aikin a yau.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 87

Idin Ketarewa na Karshe da Yesu Ya Yi

Yesu ya koya wa mabiyansa wani darasi mai muhimmanci a lokacin da yake yin idi na karshe.

DARASI NA 88

An Kama Yesu

Yahuda ya zo da sojoji rike da makamai don su kama Yesu.

DARASI NA 89

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

Mene ne ya faru a gidan Kayafa? Mene ne aka yi wa Yesu a gidan Kayafa?

DARASI NA 90

Yesu Ya Mutu a Golgota

Me ya sa Ba-bunti ya ce a kashe Yesu?

DARASI NA 91

Allah Ya Tayar da Yesu Daga Matattu

Wadanne abubuwan ban mamaki ne suka faru bayan an kashe Yesu?

DARASI NA 92

Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi

Mene ne Yesu ya yi don ya jawo hankalinsu wurinsa?

DARASI NA 93

Yesu Ya Koma Sama

Kafin ya koma sama, ya ba wa almajiransa shawarwari masu kyau.