Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 84

Yesu Ya Yi Tafiya a Kan Teku

Yesu Ya Yi Tafiya a Kan Teku

Ba ƙarfin warkar da marasa lafiya da kuma ta da matattu kawai Yesu yake da shi ba, amma yana da iko a kan iska da ruwa. Bayan Yesu ya yi addu’a a kan dutse, sai ya ga ana iska mai ƙarfi a Tekun Galili. Manzanninsa suna cikin jirgin suna fama. Sai Yesu ya sauko daga tudun kuma ya soma tafiya a kan ruwan tekun. Ya nufi wurin manzanninsa. Sa’ad da suka ga mutum yana tafiya a kan ruwa, sai suka ji tsoro. Amma Yesu ya ce musu: ‘Ni ne. Kada ku ji tsoro.’

Sai Bitrus ya ce: ‘Ubangiji, idan kai ne da gaske, ka ce in zo wurinka.’ Yesu ya ce wa Bitrus: ‘Ka zo.’ Sai Bitrus ya sauko daga jirgin, ya soma zuwa wurin Yesu. Amma sa’ad da ya kusa da Yesu, sai ya kalli iskar kuma ya ji tsoro, ya soma nitsewa. Bitrus ya yi ihu, ya ce: ‘Ubangiji, ka cece ni!’ Yesu ya riƙe hannunsa, ya ce: ‘Me ya sa ka soma shakka? Ina bangaskiyarka take?’

Sai Yesu da Bitrus suka shiga jirgin, kuma nan da nan iskar ta tsaya. Ka yi tunanin yadda manzannin suka ji? Sun ce: “Hakika, kai Ɗan Allah ne.”

Ba a wannan lokaci ne kaɗai Yesu ya nuna iko a kan iska ba. Amma akwai lokacin da manzanninsa suke tsallake teku, sai Yesu ya soma barci a cikin jirgin. Sa’ad da yake barci, sai aka soma iska mai ƙarfi. Iskar ta soma nitsar da jirgin. Manzannin suka ta da Yesu daga barci, da ihu suna cewa: ‘Malam, za mu mutu! Ka taimake mu!’ Sai Yesu ya farka daga barci kuma ya ce wa tekun: “Ka natsu!” Nan da nan iskar ta tsaya kuma tekun ya natsu. Yesu ya tambayi manzanninsa cewa: ‘Ina bangaskiyarku take?’ Sai suka ce wa juna: “Har iska da teku suna biyayya da shi.” Manzannin sun koya cewa ba sa bukatar su ji tsoro idan sun dogara ga Yesu.

“Da ina ne zan kasance, da ban gaskata cewa zan ga alherin Jehobah a cikin ƙasa ta masu rai ba?”​—Zabura 27:​13, New World Translation