Muna gayyatarka ka halarci taron yanki na kwana uku da Shaidun Jehobah za su yi bana.

ABUBUWAN DA ZA A YI A WANNAN TARON SU NE

  • Jawabai da Ganawa: Za ka koyi yadda za ka iya fuskantar matsaloli a yanzu da kuma a nan gaba ba tare da jin tsoro ba.

  • Hotuna da Sauti da Kananan Bidiyoyi: Za ka koyi karfin zuciya daga mutane da kuma dabbobi.

  • Jawabi na Musamman: Za ka san abin da ya sa Yesu ya gaya ma wani mahaifin da ‘yarsa ta rasu cewa: “Kada ka ji tsoro.” (Markus 5:36) Ka kasa kunne sosai yayin da ake ba da jawabi daga Littafi Mai Tsarki a ranar Lahadi da safe. Jigon jawabin shi ne, “Ta Yaya Begen Tashin Matattu Zai Sa Mu Kasance da Karfin Zuciya?”

  • Fim: A ranar Lahadi da rana, za ka ga abin da ya sa Yunana ya ji tsoro kuma ya gudu sa’ad da Allah ya ba shi aiki.

WA ZAI IYA HALARTAN TARON?

Kowa. Kyauta ake shiga kuma ba a yawo da tire don karban kudi.

Za ka sami cikakken tsarin ayyuka na wannan taron kuma za ka iya kallon bidiyo game da manyan taronmu.