Koma ka ga abin da ke ciki

Taron Tunawa da Mutuwar Yesu

Lahadi, 24 ga Maris, 2024

Sau daya a shekara, Shaidun Jehobah a fadin duniya suna tunawa da mutuwar Yesu. Muna yin hakan ne domin Yesu ya umurci mabiyansa cewa: “Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”—Luka 22:19.

Muna gayyatar ka ka zo wannan taron.

Tambayoyin da Ake Yawan Yi

Taron zai dau tsawon wane lokaci?

Taron wajen awa daya ne.

A ina ne za a yi taron?

Ka tambayi Shaidun Jehobah da suke kusa da kai.

Ana biyan kudi kafin a shiga?

Aꞌa.

Za a karbi baiko?

Aꞌa. Shaidun Jehobah ba sa karban baiko a taronsu.

Wane irin kayan ne zan saka don zuwa taron?

Ko da yake ba wani irin kaya da aka zaba don zuwa taron nan, Shaidun Jehobah suna iya kokari su bi shawarar Littafi Mai Tsarki game da saka rigunan da suka dace. (1 Timoti 2:9) Ba sai ka saka riguna masu tsada ba.

Me za a yi a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

Ana fara taron da waka da adduꞌa kuma a rufe da waka da kuma adduꞌa. Wani Mashaidin Jehobah ne zai yi adduꞌar. Abu na musamman da ake yi a taron shi ne jawabi da zai bayana abin da ya sa mutuwar Yesu yake da muhimmanci, da kuma yadda za mu amfana daga wannan abin da Allah da Yesu suka yi mana.