Koma ka ga abin da ke ciki

Taron Ikilisiya na Shaidun Jehobah

Ka koya game da taronmu. Ka nemi wajen taro mafi kusa da kai.

Ka Nemi Wurin da ke Kusa da Kai (opens new window)

Me Muke Yi a Taronmu?

Shaidun Jehobah suna zuwa taro sau biyo kowane mako don su bauta wa Allah. (Ibraniyawa 10:24, 25) A waɗannan taron da kowane mutumi zai iya halarta, muna bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya ce da kuma yadda za mu yi amfani da shi a rayuwarmu.

Yawancin jawaban da ake yi sun ƙunshi tambayoyi da amsoshin waɗanda masu sauraro za su amsa, kamar yadda ake yi a cikin aji. Muna fara taron da waƙa tare da addu’a, kuma a rufe taron da waƙa da addu’a.

Ba lallai sai ka zama Mashaidi ba kafin ka halarci taronmu. Muna gayyatar kowa ya zo. Ba a biyan ko sisi Kuma ba ma karɓan baiko.