Koma ka ga abin da ke ciki

Yaya Tsarin Ikilisiyarku Yake?

Yaya Tsarin Ikilisiyarku Yake?

 Rukunin dattawa suke kula da kowace ikilisiya. Aƙalla ikilisiyoyi 20 suke cikin da’ira, kuma da’ira 10 suke cikin gunduma. Jifa jifa dattawa masu ziyara da ake ce da su masu kula da da’ira kuma masu kula da gunduma suna ziyartar ikilisiyoyi.

 Ja-gora daga Littafi Mai Tsarki yana fitowa ne daga Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, waɗanda Shaidun Jehobah ne da suka daɗe suna hidima, kuma a yanzu suna Hedkwatar Shaidun Jehobah da ke Brooklyn, New York.—Ayyukan Manzani 15:23-29; 1 Timothawus 3:1-7.