Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 51

Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya

Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya

Da akwai wata yarinya ’yar Isra’ila a ƙasar Suriya. Ƙasar Suriya na da nisa sosai daga Isra’ila. Sojojin Suriya ne suka ɗauke ta daga wurin iyayenta kuma ta zama baiwa ga matar wani babban soja mai suna Na’aman. Ko da yake mutanen Suriya ba sa bauta wa Jehobah, wannan yarinyar ta ci gaba da bauta wa Jehobah.

Na’aman yana da wata mummunar cuta kuma cutar tana da zafi sosai. Yarinyar tana so ta taimaka masa. Sai ta gaya wa matar Na’aman cewa: ‘Akwai wani da na sani a Isra’ila da zai iya warkar da maigidanki. Shi annabin Jehobah ne kuma sunansa Elisha.’

Matar Na’aman ta gaya masa abin da yarinyar ta gaya mata. Na’aman yana a shirye ya yi kome don ya sami sauƙi. Don haka, ya je gidan Elisha a Isra’ila. Na’aman ya ɗauka cewa Elisha zai girmama shi fiye da sauran mutane. Amma Elisha bai fito ya yi magana da shi ba. Maimakon haka, ya tura bawansa ya gaishe Na’aman kuma ya ce masa: ‘Ka je ka yi wanka a cikin Kogin Urdun sau bakwai. Bayan haka za ka warke.’

Hakan ya sa Na’aman fushi sosai. Sai ya ce: ‘Na zata cewa wannan annabin zai kira sunan Allahnsa kuma ya warkar da ni. Maimakon haka, ya ce in je kogin da ke Isra’ila. Kogunanmu a Suriya sun fi nasu kyau. Zai fi kyau in je na ƙasarmu.’ Sai Na’aman ya bar gidan Elisha da fushi.

Amma bayin Na’aman sun taimaka masa ya yi tunani sosai. Sun ce masa: ‘Ba ka ce za ka iya yin kome don ka warke ba? Abin da wannan annabin ya gaya maka ba shi da wuya. Me ya sa ba za ka yi ba?’ Na’aman ya saurari abin da suka gaya masa. Sai ya tafi Kogin Urdun kuma ya yi wanka sau bakwai. Bayan da ya yi na bakwan, sai Na’aman ya warke. Ya yi farin ciki sosai kuma ya koma wurin Elisha don ya gode masa. Na’aman ya ce: ‘Yanzu na san cewa Jehobah shi ne Allah na gaskiya.’ Yaya kake ganin wannan yarinyar ’yar Isra’ila ta ji da Na’aman ya dawo gida a warke?

‘Daga cikin bakin jarirai da masu-shan mama ka cika yabo.’​—Matta 21:16