Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 57

Jehobah Ya Aiki Irmiya Ya Yi Wa’azi

Jehobah Ya Aiki Irmiya Ya Yi Wa’azi

Jehobah ya zaɓi Irmiya ya zama annabi ga Yahudawa. Ya gaya masa cewa ya yi wa mutanen wa’azi kuma ya gaya musu cewa su daina yin abubuwa marasa kyau. Amma Irmiya ya ce: ‘Jehobah ni ƙaramin yaro ne. Ban san yadda zan yi wa mutanen magana ba.’ Sai Jehobah ya gaya masa: ‘Kada ka ji tsoro. Zan gaya maka abin da za ka ce. Zan taimake ka.’

Jehobah ya gaya wa Irmiya ya tattara dattawan ƙasar, ya fasa tulu a gabansu kuma ya gaya musu cewa: ‘Haka za a rushe Urushalima.’ Da Irmiya ya yi abin da Jehobah ya gaya masa, sai dattawan suka yi fushi sosai. Wani firist mai suna Pashhur ya yi wa Irmiya dūka kuma ya maƙale hannuwansa da ƙafafunsa a wani katako. Irmiya ya kasa motsawa har gari ya waye. Pashhur ya sake shi washegari. Sai Irmiya ya ce: ‘Ya isa haka. Ba zan ƙara yin wa’azi ba.’ Amma sa’ad da Irmiya ya yi tunani a kan batun, sai ya ce: ‘Maganar Allah kamar wuta take a cikin jikina. Ba zan daina yin wa’azi ba.’ Irmiya ya ci gaba da yi wa mutanen wa’azi.

Bayan shekaru da yawa, sai Yahudawa suka yi sabon sarki. Firistoci da kuma annabawan ƙarya sun tsani abin da Irmiya yake cewa. Sai suka gaya wa hakimai cewa: ‘Ya kamata a kashe wannan mutumin.’ Amma Irmiya ya ce: ‘Idan kuka kashe ni, kun kashe marar laifi. Abin da nake faɗa ba nawa ba ne amma na Jehobah ne.’ Da hakiman suka ji hakan, sai suka ce: ‘Bai kamata a kashe wannan mutumin ba.’

Irmiya ya ci gaba da yin wa’azi kuma hakan ya sa hakiman fushi sosai. Sai suka gaya wa sarkin cewa ya kashe Irmiya. Hakan ya sa  sarkin ya gaya musu cewa su yi wa Irmiya duk abin da suka ga dama. Sai suka ɗauki Irmiya kuma suka jefa shi cikin wata babbar rijiya da ke cike da taɓo don ya mutu a ciki. A hankali, Irmiya ya soma nitsewa a cikin taɓon.

Ana cikin haka, sai Ebed-melek wanda ma’aikaci ne a fādar ya gaya wa sarkin cewa: ‘Hakimai sun saka Irmiya a cikin rijiya! Zai mutu idan aka bar shi a wurin.’ Nan da nan sarkin ya umurci Ebed-melek cewa ya tafi da mutane 30 don su fitar da Irmiya daga rijiyar. Ya kamata mu yi koyi da Irmiya wanda ya ƙi daina yin wa’azi duk da hamayya, ko ba haka ba?

“Za ku zama abin ƙi ga dukan mutane sabili da sunana: amma wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.”​—Matta 10:22