Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 31

Joshua da Gibeyonawa

Joshua da Gibeyonawa

Labarin abin da ya same Yariko ya bazu a duk cikin ƙasar Kan’ana. Sarakunan sun haɗa baki domin su yaƙi Isra’ilawa. Amma sai Gibeyonawan suka kawo wata dabara dabam. Sun sanya tsofaffin kaya kuma suka je wurin Joshua, suka ce masa: ‘Daga wata ƙasa mai nisa muka fito. Mun ji labarin Jehobah da kuma dukan abubuwan da ya yi muku a ƙasar Masar da Mowab. Za mu zama bayinku idan kun yi mana alkawari cewa ba za ku kashe mu ba.’

Joshua ya yarda da su kuma ya ce ba zai kashe su ba. Amma bayan kwana uku, sai ya ji cewa ƙarya suka yi masa da suka ce wai daga ƙasa mai nisa suka fito. Su ’yan ƙasar Kan’ana ne. Sai Joshua ya tambaye su: ‘Me ya sa kuka yi mana ƙarya?’ Sai suka ce: ‘Mun ji tsoro ne! Mun san cewa Jehobah Allahnku yana tare da ku. Don Allah kar ku kashe mu.’ Joshua bai kashe su ba.

Kafin ka sani, sai sarakuna biyar daga ƙasar Kan’ana tare da sojojinsu suka ce za su kashe Gibeyonawa. Joshua da sojojinsa ba  su yi barci ba a daren don sun tafi su ceci Gibeyonawan. Sai suka fara faɗa washegari da sassafe, kuma Kan’aniyawan suka soma guduwa. Amma duk inda suka je, Jehobah yana ta harbinsu da ƙanƙara. Sai Joshua ya roƙi Jehobah ya sa rana ta tsaya cak. Me ya sa zai yi irin wannan roƙon tun da yake ba a taɓa ganin rana ta tsaya cak ba? Ya yi hakan ne don ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah sosai. Kuma rana ta tsaya cak har sai da Isra’ilawa suka ci sarakuna da kuma sojojin Kan’aniyawa da yaƙi.

“Abin da duk za ku faɗa, ya tsaya kan ‘I’ ko ‘A’a’ kawai. In dai ya zarce haka, daga Mugun ya fito.”​—Matta 5:​3, Littafi Mai Tsarki