Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 44

Haikalin Jehobah

Haikalin Jehobah

Bayan Sulemanu ya zama sarkin Isra’ila, sai Jehobah ya tambaye shi: ‘Mene ne kake so in ba ka?’ Sai Sulemanu ya ce: ‘Ni matashi ne, ban san abin da nake yi ba. Ka ba ni hikima don in ja-goranci mutanenka.’ Sai Jehobah ya ce: ‘Da yake ka ce in ba ka hikima, zan sa ka zama mutum mafi hikima a dukan duniya. Kuma zan sa ka zama mai arziki sosai. Idan ka bi umurnina, za ka yi tsawon rai.’

Sai Sulemanu ya soma gina haikalin. Ya yi amfani da zinariya da azurfa da katako da kuma duwatsu mafi kyau. Dubban maza da mata da suka ƙware sosai ne suka gina haikalin. An gama ginin bayan shekara bakwai kuma aka yi shirin keɓe ta ga Jehobah. Haikalin yana da wurin ƙona hadaya, wato bagadi kuma akwai hadaya a kan bagadin. Sulemanu ya durƙusa a gaban bagadin kuma ya yi addu’a cewa: ‘Ya Jehobah, girman haikalin nan da kuma kyaunsa, ba zai ishe ka ba, amma muna roƙon ka ka amince da ibadarmu kuma ka ji addu’o’inmu.’ Yaya Jehobah ya ji game da haikalin da kuma addu’ar da Sulemanu ya yi? Bayan Sulemanu ya gama addu’ar, nan da nan sai wuta ta fito daga sama ta cinye hadayar da ke kan bagadin. Jehobah ya amince da haikalin. Hakan ya sa Isra’ilawan murna sosai.

Dukan Isra’ilawa da kuma mutane daga wurare masu nisa sun ji cewa Sarki Sulemanu yana da hikima sosai. Mutane suna zuwa wurin Sulemanu don ya yi maganin matsalolinsu. Har ma sarauniyar Sheba ta zo wurinsa don ta yi masa tambayoyi masu wuya. Da ta ji amsoshin da ya ba ta, sai ta ce: ‘A dā ban yarda da abin da mutane suke cewa game da kai ba, amma yanzu na ga cewa kana da hikima fiye da yadda ma suka faɗa. Allahnka Jehobah ya albarkace ka.’ Isra’ilawa sun ji daɗin rayuwa kuma sun yi farin ciki sosai. Amma abubuwa za su canja.

‘Ga kuwa wanda ya fi Sulemanu girma a nan.’​—Matta 12:42