Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 67

Ganuwar Urushalima

Ganuwar Urushalima

Akwai wani Ba’isra’ile mai suna Nehemiya a zamanin Ezra wanda shi bawan Sarki Artaxerxes ne. Yana zama a birnin Shushan a ƙasar Fasiya. ’Yan’uwan Nehemiya sun zo daga Urushalima kuma suka ce masa: ‘Mutanen da suka koma Urushalima suna cikin haɗari. Har yanzu ba a gina ganuwar birnin da mutanen Babila suka halaka ba.’ Hakan ya sa Nehemiya baƙin ciki sosai. Yana so ya je Urushalima don ya taimaka musu. Don haka, ya roƙi Allah ya sa sarkin ya bar shi ya tafi.

Wata rana, sarkin ya lura cewa Nehemiya ba ya farin ciki. Sai ya ce masa: ‘Ban taɓa ganin ka a cikin wannan yanayin ba. Mene ne yake damunka?’ Nehemiya ya ce: ‘Ina baƙin ciki ne domin birninmu Urushalima yana cikin haɗari.’ Sai sarkin ya ce masa: ‘Me kake so in yi maka?’ Nan da nan Nehemiya ya yi addu’a a cikin zuciyarsa. Bayan ya gama addu’ar, sai ya ce: ‘Don Allah ka bar ni in tafi Urushalima don in sake gina ganuwar.’ Sai Sarki Artaxerxes ya ba Nehemiya izini kuma ya yi masa tanadi don tafiyarsa. Ƙari ga haka, ya naɗa Nehemiya gwamnar Yahuda kuma ya ba shi katakon da zai yi ƙofar birnin da shi.

Da Nehemiya ya isa Urushalima, sai ya je ya duba ganuwar birnin. Bayan haka, sai ya tara firistoci da shugabanni kuma ya ce musu: ‘Muna cikin matsala. Muna bukatar mu soma aiki nan da nan.’ Sai mutanen suka amince kuma suka soma gina ganuwar.

Amma sai maƙiyan Isra’ilawa suka soma yi musu dariya suna cewa: ‘Dila zai iya rushe wannan ginin da kuke yi.’ Amma ma’aikatan ba su saurare su ba kuma suka ci gaba da ginin.

Sai maƙiyan suka yanke shawara cewa za su bi ta wata hanya dabam don su kai wa Urushalima hari a lokacin da ba su zata ba. Da Yahudawan suka ji haka, sai tsoro ya kama su. Amma Nehemiya ya ce musu: ‘Kada ku ji tsoro. Jehobah yana tare da mu.’ Sai Nehemiya ya sa wasu mutane su riƙa yin gadin masu aikin kuma hakan ya sa maƙiyan ba su iya kai musu hari ba.

An gama gina ganuwar da kuma ƙofar a cikin kwana 52. Sai Nehemiya ya tattara dukan Lawiyawan Urushalima don a yi biki. Ya raba su zuwa rukuni biyu na mawaƙa. Sai mawaƙan suka hau ganuwar ta wurin matakalai da ke Ƙofar Maɓulɓular Ruwa kuma suka zagaye birnin gabaki ɗaya. Sun yi amfani da ƙahoni da kuge da molo da kuma giraya don su rera waƙa ga Jehobah. Ezra ya ja-goranci wani rukuni, Nehemiya kuma ya ja-goranci ɗayan rukunin har suka zo suka haɗu a cikin haikalin. Dukansu maza da mata da yara sun miƙa hadaya ga Jehobah kuma suka yi biki. An ji muryoyinsu daga can nesa saboda farin cikin da suke yi.

“Ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki.”​—Ishaya 54:​17, Littafi Mai Tsarki