Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 7

Hasumiyar Babel

Hasumiyar Babel

Bayan Ambaliyar Ruwan, yaran Nuhu sun haifi yara da yawa. Sai suka soma yawa kuma suka soma zama a wurare dabam-dabam a duniya, kamar yadda Jehobah ya ce su yi.

Amma wasu daga cikin jikokin Nuhu ba su yi biyayya ga Jehobah ba. Sun ce: ‘Bari mu gina birni kuma mu zauna a ciki. Za mu gina babban gida wanda tsawonsa zai kai sama. Haka zai sa a san mu sosai.’

 Abin da mutanen suka yi ya sa Jehobah fushi, sai ya ce zai hana su yin ginin. Ka san yadda ya yi hakan? Ya sa sun soma yin yare dabam-dabam. Tun da ba su fahimci juna ba, sai suka daina ginin. Birnin da suka gina ne ake kira Babel, wato “Ruɗewa.” Sai mutanen suka soma zama a ƙasashe dabam-dabam. Amma sun ci gaba da yin abubuwa marar kyau a waɗannan wuraren. Kana ganin da akwai mutumin da ke ƙaunar Jehobah a duniya a lokacin? Za mu sami amsar a babi na gaba.

“Allah yana ƙin mai girman kai, amma yana yin alheri ga mai sauƙin kai.”​—Yaƙub 4:​6, Juyi Mai Fitar da Ma’ana