Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 54

Jehobah Ya Yi Hakuri da Yunana

Jehobah Ya Yi Hakuri da Yunana

Assuriyawa da ke birnin Nineba suna yin abubuwa marasa kyau sosai. Jehobah ya aiki annabinsa mai suna Yunana cewa ya je Nineba kuma ya gaya wa mutanen su daina abubuwa marasa kyau da suke yi. Amma Yunana ya gudu ya tafi wani wuri dabam. Ya je ya shiga jirgin da zai kai shi birnin Tarshish.

Da suke cikin tafiya, sai aka soma wata iska mai ƙarfi sosai kuma masu tuƙa jirgin suka soma jin tsoro. Sai suka soma addu’a ga allolinsu kuma suka yi tambaya cewa: ‘Mene ne yake faruwa?’ Daga ƙarshe, sai Yunana ya ce: ‘Ni ne da laifi. Na ƙi yin abin da Jehobah ya gaya mini na yi. Ku jefa ni cikin tekun kuma iskar za ta tsaya.’ Masu tuƙa jirgin ba su so su jefa shi ba amma Yunana ya nace. Da suka jefa Yunana cikin tukun, sai aka daina iskar.

Yunana ya ɗauka cewa zai mutu. Da yake nitsewa cikin tekun, sai ya yi addu’a ga Jehobah. Jehobah ya tura wani babban kifi. Kifin ya haɗiye Yunana amma bai kashe shi ba. Yunana ya sake yin addu’a sa’ad da yake cikin kifin cewa: ‘Na yi alkawari cewa zan riƙa yi maka biyayya a koyaushe.’ Yunana ya yi kwana uku a cikin kifin kuma Jehobah ya kāre shi. Daga baya, Jehobah ya sa kifin ya yi amansa a bakin tekun.

Tun da Jehobah ya ceci Yunana, hakan yana nufin cewa ba ya bukatar ya je Nineba kuma? A’a. Jehobah ya sake gaya wa  Yunana cewa ya je birnin. A wannan lokacin, Yunana ya saurari Allah. Ya je wurin kuma ya gaya wa mugayen mutanen cewa: ‘Za a halaka Nineba a cikin kwana 40.’ Sai wani abin mamaki ya faru. Mutanen Nineba sun saurara kuma suka canja halayensu. Sarkin Nineba ya gaya wa mutanen cewa: ‘Ku roƙi Allah kuma ku tuba. Wataƙila ba zai halaka mu ba.’ Da Jehobah ya ga cewa mutanen sun tuba, sai ya yafe musu.

Da Yunana ya ga cewa ba a halaka birnin ba, sai ya yi fushi. Jehobah ya yi haƙuri sa’ad da yake sha’ani da Yunana kuma ya ji tausayin sa, amma Yunana bai ji tausayin mutanen Nineba ba. Maimakon haka, ya zauna a wajen birnin a ƙarƙashin itacen duma yana jira Jehobah ya halaka mutanen. Daga baya, sai itacen ya mutu kuma hakan ya sa Yunana fushi sosai. Jehobah ya ce wa Yunana: ‘Ka damu da wannan itacen fiye da mutanen Nineba. Na ji tausayin su, shi ya sa suka tsira.’ Mene ne darasin? Mutanen Nineba sun fi kowane irin itace daraja sosai.

Jehobah “mai haƙuri ne zuwa gare ku, ba shi nufin kowa da halaka ba, amma duka su kai ga tuba.”​—2 Bitrus 3:9