Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 46

Jehobah Ne Allah Na Gaskiya

Jehobah Ne Allah Na Gaskiya

Ƙabila goma na Isra’ila na da mugayen sarakuna da yawa, amma Ahab ya fi dukansu mugunta. Ya auri wata muguwar mace mai bautar Baal. Sunanta Jezebel. Ahab da Jezebel sun cika ƙasar da bautar Baal kuma sun kashe annabawan Jehobah. Mene ne Jehobah ya yi? Ya aika annabi Iliya wajen Ahab.

Iliya ya gaya wa Sarki Ahab cewa ba za a yi ruwan sama ba a Isra’ila don muguntarsa. Sun yi shekaru uku ba su yi noma ba kuma hakan ya jawo yunwa sosai. Sai Jehobah ya sake aika Iliya wajen Ahab. Sarkin ya ce: ‘Kai mai rigima ne! Kai ka jawo wannan matsalar.’ Sai Iliya ya ce: ‘Ba ni ba ne na jawo matsalar ba. Kai ne ka jawo hakan domin kana bauta wa Baal. Za mu yi wani gwaji. Ka tattara mutanen gabaki ɗaya da kuma annabawan Baal a kan Dutsen Karmel.’

Sai mutanen suka taru a kan dutsen. Iliya ya ce: ‘Ku yi zaɓi yanzu. Idan Jehobah ne Allah na gaskiya, ku bauta masa. Amma idan Baal ne, sai ku bauta masa. Ina so waɗannan annabawan Baal guda 450 su yi hadaya kuma su yi addu’a ga allahnsu. Ni ma zan yi hadaya kuma in yi addu’a ga Jehobah. Duk Allahn da ya amsa ta wajen aiko da wuta, shi ne Allah na gaskiya.’ Sai mutanen suka yarda.

Annabawan Baal ɗin suka shirya hadaya. Suka wuni suna kiran allahnsu: ‘Ya Baal, ka ji addu’armu!’ Da yake Baal bai amsa ba, sai Iliya ya soma musu dariya. Ya ce: ‘Ku ɗaga muryarku sosai. Wataƙila barci ya kwashe shi, kuma yana bukatar a tashe shi.’ Annabawan suka ci gaba da kira har yamma. Amma sun ji shiru kamar an shuka dusa.

Sai Iliya ya ajiye hadayarsa a kan bagadi kuma ya zuba ruwa a kai. Bayan haka, ya yi addu’a: ‘Ya Jehobah, ina roƙo, ka sa mutanen nan su san cewa kai ne Allah na gaskiya.’ Nan da nan, sai Jehobah ya aiko da wuta daga sama kuma ta cinye hadayar. Sai mutanen suka yi ihu:  ‘Jehobah shi ne Allah na gaskiya!’ Iliya ya ce: ‘Kada ku bar annabawan Baal ɗin su gudu!’ Suka kashe dukan annabawan guda 450 a ranar.

Bayan wani lokaci, sai aka sake soma yin ruwa. Iliya ya ga ƙaramin gajimare a sama, sai ya ce wa Ahab: ‘Za a yi ruwa sosai. Ka hau karusarka ka koma gida.’ Sai gari ya yi duhu kuma aka soma iska da ruwa. Ahab ya yi gudu sosai da karusarsa amma Iliya ya yi gudu da kafa. Da taimakon Jehobah, Iliya ya wuce shi! Shin Iliya ya sami sauƙi ga dukan matsalolinsa kuwa? Bari mu gani.

‘Domin su sani kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’​—Zabura 83:18