Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 8

Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah

Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah

Akwai wani birni mai suna Ur kuma wannan birnin bai da nisa daga Babel. Mutanen birnin ba sa bauta wa Jehobah. Amma akwai wani mutumi mai suna Ibrahim a birnin Ur da ke bauta wa Jehobah kaɗai.

Jehobah ya ce wa Ibrahim: ‘Ka fita daga ƙasarka da kuma mutanenka zuwa ƙasar da zan nuna maka.’ Sai Allah ya yi masa alkawari cewa: ‘Yaranka za su yi yawa sosai, kuma dukan mutanen duniya za su sami albarka saboda kai.’

Ko da yake Ibrahim bai san inda Jehobah ya ce ya je ba, amma ya nuna bangaskiya. Sai Ibrahim da matarsa Saratu da babansa  Terah da kuma Lutu yaron ɗan’uwan Ibrahim suka kwashe kaya, suka soma tafiya mai nisa.

Shekarun Ibrahim 75 ne sa’ad da shi da iyalinsa suka isa inda Jehobah ya ce su je. Sunan ƙasar Kan’ana. Sai Allah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa: ‘Zan ba yaranka duka wannan ƙasa da ta kewaye ka.’ Amma Ibrahim da Saratu sun tsufa kuma ba su da yara. To, ta yaya Jehobah zai cika wannan alkawarin?

“Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim ya yi biyayya ya kama hanya zuwa wata ƙasa wadda aka yi masa alkawari cewa zai karɓi gādonta. Shi kuwa ya kama hanya ko da bai san inda za shi ba.”​—Ibraniyawa 11:​8, Juyi Mai Fitar da Ma’ana