Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 89

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu

Sa’ad da Yesu yake tare da manzanninsa a ɗakin da ke wani gidan sama, ya gaya musu cewa: ‘A daren nan, dukanku za ku gudu ku bar ni.’ Sai Bitrus ya ce: ‘Ban da ni! Idan dukansu za su gudu su bar ka, ni ba zan bar ka ba.’ Amma Yesu ya gaya masa cewa: ‘Kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sani na sau uku.’

Duka manzannin sun gudu sa’ad da sojojin suka kai Yesu gidan Kayafa. Amma Bitrus da wani almajirin Yesu sun bi mutanen. Sai Bitrus ya shiga gidan Kayafa yana jin ɗumi a gefen wuta. A wajen ne wata baiwa ta ga fuskar Bitrus kuma ta ce: ‘Na san ka! Kai ma kana tare da Yesu!’

Bitrus ya ce: ‘A’a, ba ni ba ne! Ban san abin da kike cewa ba.’ Sai ya kama hanya zuwa bakin ƙofa. Amma sai wata baiwa kuma ta gan shi kuma ta gaya wa mutane cewa: ‘Wannan mutumin ma yana tare da Yesu!’ Bitrus ya ce: ‘Ban san Yesu ba!’ Sai wani mutum ya sake cewa: ‘Kana cikinsu! Yadda kake magana ya sa na gane cewa kai ɗan Galili ne kamar Yesu.’ Amma Bitrus ya rantse cewa: ‘Ban san shi ba!’

A wannan lokacin, sai zakara ya yi cara. Bitrus ya ga sa’ad da Yesu ya juya kuma ya kalle shi. Sai ya tuna da abin da Yesu ya ce kuma ya fita waje ya yi kuka sosai.

’Yan Majalisar Yahudawa sun taru a gidan Kayafa don su yi wa Yesu tambayoyi. Sun riga sun yanke shawara cewa za su kashe shi amma ba su da hujjar yin hakan. A ƙarshe, sai Kayafa ya tambayi Yesu kai tsaye cewa: ‘Shin kai ne Ɗan Allah?’ Yesu ya ce: ‘E, ni ne.’ Kayafa ya ce: ‘Ba ma bukatar wasu hujjoji. Wannan ai saɓo yake yi!’ Sai mutanen suka amince cewa: ‘A kashe wannan mutum.’ Sun mari Yesu, sun tofa masa yau, sun rufe masa idanu kuma suka dūke shi suna cewa: ‘Idan kai annabi ne, ka gaya mana wanda ya dūke ka!’

Da gari ya waye, sai suka kai Yesu wurin da ’yan Majalisa suke yin taronsu kuma suka tambaye shi: ‘Kai Ɗan Allah ne?’ Sai Yesu ya ce: ‘Ku ma kuna faɗin hakan.’ Bayan haka, sai suka ce Yesu yana saɓo kuma suka kai shi wurin gwamnan Romawa mai suna Bilatus Ba-bunti. Mene ne ya faru bayan haka? Bari mu gani.

“Sa’a . . . ta zo, inda za ku warwatse, kowa zuwa nasa, za ku bar ni ni kaɗai: amma ba ni ɗaya ba ne, gama Uba yana tare da ni.”​—Yohanna 16:32