Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 60

Gwamnatin da Za ta Yi Sarauta Har Abada

Gwamnatin da Za ta Yi Sarauta Har Abada

Wata rana daddare, Sarki Nebuchadnezzar ya yi mafarki. Abin da ya gani ya dame shi sosai har ya kasa barci. Sai ya kira mutanensa masu hikima, ya ce: ‘Ku bayyana mini mafarkin da na yi.’ Sai suka ce masa: ‘Ya sarki, ka gaya mana mafarkin da ka yi.’ Amma Nebuchadnezzar ya gaya musu: ‘A’a! Ku gaya mini mafarkin da na yi, in ba haka ba, zan kashe ku.’ Sai suka sake gaya masa: ‘Ka fara gaya mana mafarkinka, mu kuma za mu bayyana maka abin da yake nufi.’ Sai ya ce: ‘Dukanku kuna so ku yi mini wayo. Ku gaya mini abin da na yi mafarkin sa!’ Sai suka gaya wa sarkin cewa: ‘Babu wani mutumin da zai iya yin haka, abin da ka ce mu yi ba zai taɓa yiwu ba.’

Nebuchadnezzar ya yi fushi sosai har ya ce a kashe dukan masu hikima da ke ƙasar. Har da Daniyel da Shadrach da Meshach da kuma Abednego. Daniyel ya ce wa sarkin ya ba su ɗan lokaci. Sai shi da abokansa uku suka yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka musu. Mene ne Jehobah ya yi?

A wahayi, Jehobah ya nuna wa Daniyel mafarkin da Nebuchadnezzar ya yi da kuma abin da yake nufi. Washegari, sai Daniyel ya je ya sami bawan sarkin kuma ya ce: ‘Kada ka kashe masu hikimar. Zan iya bayyana mafarkin sarkin.’ Sai bawan ya kai Daniyel gaban Nebuchadnezzar. Daniyel ya ce wa sarki: ‘Allah ya nuna maka abin da zai faru a nan gaba. Ga abin da ka yi mafarkin sa: Ka ga wani babban gunki da ke da kan zinariya, ƙirjinsa da kuma hannayensa na azurfa, cikinsa da kuma cinyoyinsa na jan ƙarfe, ƙafafunsa na ƙarfe, sawayensa kuma na ƙarfe haɗe da laka. Sai wani dutse ya faɗo daga wani tudu ya bugi ƙafafun gunkin. Sai gunkin ya farfashe  kuma iska ta watsar da shi. Wannan dutsen ya zama wani babban tudu kuma ya cika duniya gabaki ɗaya.’

Sai Daniyel ya ce: ‘Ga abin da mafarkinka yake nufi: Kan gunkin na zinariya yana wakiltar sarautarka. Azurfar tana wakiltar mulkin da zai biyo bayanka. Bayan haka, za a yi gwamnatin da take kama da jan ƙarfe da za ta yi sarauta a dukan duniya. Sai kuma gwamnati da ke da ƙarfi kamar ƙarfe. A ƙarshe, za a yi mulkin da ba zai sami haɗin kai ba, wani ɓangare zai yi ƙarfi kamar ƙarfe, wani kuma kamar laka. Wannan dutsen da ya zama babban tudu yana wakiltar Mulkin Allah. Zai halaka dukan mulkokin duniyar nan kuma zai yi sarauta har abada.’

Sai Nebuchadnezzar ya faɗi a gaban Daniyel kuma ya ce: ‘Allahnka ne ya bayyana maka wannan mafarkin. Babu wani Allah kamarsa.’ Maimakon ya kashe Daniyel, sai Nebuchadnezzar ya mai da shi shugaban dukan masu hikima kuma ya naɗa shi sarkin lardin Babila. Ka ga yadda Jehobah ya amsa addu’ar Daniyel?

“Aka tattara su a wurin da ake ce da shi da Ibrananci Armagedon.”​—Ru’ya ta Yohanna 16:16