Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 11

An gwada bangaskiyarsa

An gwada bangaskiyarsa

Ibrahim ya koya wa yaronsa Ishaƙu cewa ya riƙa ƙaunar Jehobah kuma ya riƙa tunawa da alkawuransa. Amma a lokacin da Ishaƙu ya kusan kai ɗan shekara 25, Jehobah ya ce Ibrahim ya yi wani abu mai wuya sosai. Mene ne ya ce ya yi?

Allah ya ce wa Ibrahim: ‘Ka ɗauki yaro guda ɗaya kawai da kake da shi, ka tafi ƙasar Moriah. Ka yi hadayar ƙonawa da shi.’ Ibrahim bai san abin da ya sa Jehobah ya ce ya yi hakan ba. Amma duk da haka, ya yi biyayya ga Jehobah.

Washegari da safe, sai Ibrahim ya ɗauki Ishaƙu da bayinsa guda biyu zuwa Moriah. Bayan sun yi tafiyar kwanaki uku, sai suka soma ganin duwatsun da za su yi hadayar. Sai Ibrahim ya gaya wa bayinsa cewa su tsaya a wurin, yayin da shi da Ishaƙu za su je yin hadaya. Ibrahim ya sa itace a kan Ishaƙu, shi kuma ya ɗauki wuƙa. Sai Ishaƙu ya tambayi babansa cewa: ‘Ina ɗan ragon da za mu yi hadaya da shi?’ Ibrahim ya ce masa: ‘Ɗana, Jehobah zai yi tanadin ɗan rago.ʼ

Sa’ad da suka kai dutsen, sai suka gina wurin da za su yi hadaya. Bayan haka, sai Ibrahim ya ɗaure hannuwan Ishaƙu da ƙafafunsa kuma ya sa shi a kan wurin yin hadayar.

Ibrahim ya ciro wuƙa. Sai mala’ikan Jehobah ya yi magana daga sama, ya ce: ‘Ibrahim! Kada ka kashe saurayin. Yanzu na san cewa kana da  bangaskiya sosai tun da yake ba ka hana Allah yaronka ba.ʼ Bayan haka, sai Ibrahim ya ga wani ragon da ya maƙale a daji. Sai ya ɗauko ragon kuma ya yi hadaya da shi.

Daga ranar, Jehobah ya soma kiran Ibrahim abokinsa. Ka san abin da ya sa? Domin Ibrahim ya yi dukan abin da Jehobah ya ce ko da bai san dalilin da ya sa ba.

Jehobah ya sake maimaita alkawarinsa ga Ibrahim. Ya ce: ‘Zan albarkace ka, zan kuma sa yaranka su yi yawa.’ Hakan na nufin cewa Jehobah zai yi amfani da Ibrahim wajen kawo albarka ga mutane masu adalci.

“Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.”​—Yohanna 3:​16, Juyi Mai Fitar da Ma’ana