Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 103

Bari “Mulkinka Ya Zo”

Bari “Mulkinka Ya Zo”

Jehobah ya yi alkawari cewa: ‘Ba za a ƙara yin kuka ko ciwo ko kuma mutuwa ba. Zan share dukan hawaye da ke idanunsu kuma ba za a ƙara tunawa da dukan munanan abubuwa ba.’

Jehobah ya sa Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin domin su yi rayuwa cikin salama da kuma farin ciki. Suna bukatar su bauta masa kuma su cika duniya da yaransu. Ko da yake Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah rashin biyayya, hakan bai canja nufinsa ga duniya ba. Littafin nan ya koya mana cewa dukan alkawuran da Allah ya yi suna cika. Mulkinsa zai kawo albarka da yawa ga wannan duniya kamar yadda ya yi wa Ibrahim alkawari.

Nan ba da daɗewa ba, za a kashe Shaiɗan da aljanunsa da kuma mugayen mutane. A lokacin, kowa zai riƙa bauta wa Jehobah. Ba za mu riƙa rashin lafiya da mutuwa ba. Amma, za mu sami ƙoshin lafiya a kullum kuma za mu riƙa farin ciki. Duniya za ta zama aljanna.  Kowa zai sami wurin zama mai kyau da kuma isashen abinci. Mutane ba za su riƙa yin faɗa da juna ba, amma za su zauna lafiya. Ba za mu riƙa jin tsoron namomin daji ba kuma su ma ba za su ji tsoron mu ba.

Za mu yi murna sosai sa’ad da Jehobah ya soma tayar da matattu. Kuma za mu haɗu da mutanen da suka mutu, kamar su Habila da Nuhu da Ibrahim da Saratu da Musa da Ruth da Esther da kuma Dauda. Dukanmu za mu mayar da Duniyar nan ta zama aljanna. Za mu riƙa yin ayyukan da za su sa mu farin ciki.

Jehobah yana son ka kasance a aljanna. Zai yi maka abubuwan da ba ka taɓa tsammani ba. Bari mu riƙa kusantar Jehobah kullum kuma mu ci gaba da yin haka har abada!

“Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu.”​—Ru’ya ta Yohanna 4:11