Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 56

Josiah Yana Son Dokar Allah

Josiah Yana Son Dokar Allah

Josiah ya zama sarkin Yahuda sa’ad da yake ɗan shekara takwas. A lokacin, mutanen suna ayyukan sihiri da kuma bautar gumaka. Amma da Josiah ya kai shekara 16, ya yi ƙoƙarin sanin yadda ya kamata a bauta wa Jehobah. Da ya kai shekara 20, sai ya soma kawar da gumaka da bagadinsu a cikin ƙasar. Sa’ad da Josiah ya kai shekara 26, sai ya yi shiri don a gyara haikalin Jehobah.

Wani babban firist mai suna Hilkiya ya samo littafin da ke ɗauke da dokar Jehobah a cikin haikalin. Wataƙila wanda Musa ya rubuta da kansa ne. Sai sakataren sarkin mai suna Shaphan ya kawo wa Josiah littafin kuma ya karanta da babbar murya. Da Josiah ya saurari karatun, sai ya gane cewa mutanen sun yi shekaru da yawa suna yin abin da Jehobah ba ya so. Sai Josiah ya gaya wa Hilkiya cewa: ‘Jehobah yana fushi da mu. Ka je ka tambaye shi abin da za mu yi.’ Sai Jehobah ya gaya wa wata annabiya mai suna Huldah cewa: ‘Yahudawa sun daina bauta mini. Zan yi musu horo, amma tun da Josiah bai yi girman kai ba, hakan ba zai faru a lokacinsa ba.’

Da Sarki Josiah ya ji saƙon, sai ya shiga cikin haikalin kuma ya sa aka kira dukan mutanen ƙasar Yahuda. Sai ya karanta musu Dokokin Jehobah da babbar murya. Sarki Josiah da mutanen sun yi wa Jehobah alkawari cewa za su yi masa biyayya da dukan zuciyarsu.

 Mutanen Yahuda sun yi shekaru da yawa ba su yi Idin Ƙetarewa ba. Amma da Josiah ya karanta a cikin Dokar cewa ya kamata a riƙa yin Idin Ƙetarewa kowace shekara, sai ya gaya masu cewa: ‘Za mu yi Idin Ƙetarewa ga Jehobah.’ Sai Josiah ya soma shirya kayan da za a yi hadaya da shi kuma ya zaɓi mutanen da za su rera waƙa a haikalin. Mutanen suka yi Idin Ƙetarewa da kuma Idin Gurasa Marar Yisti har kwana takwas. Ba a taɓa yin Idin Ƙetarewa kamar haka ba tun daga lokacin Sama’ila. Hakika, Josiah yana son Dokar Allah. Kana jin daɗin koyan abubuwa game da Jehobah?

“Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma a tafarkina.”​—Zabura 119:105