Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 83

Yesu Ya Ciyar da Dubban Mutane

Yesu Ya Ciyar da Dubban Mutane

Kafin Idin Ƙetarewa na shekara ta 32 bayan haihuwar Yesu, manzanninsa sun dawo daga wa’azi kuma sun gaji sosai. Sai Yesu ya ce musu su je Baitsaida a jirgin ruwa domin su huta. Amma sa’ad da suka kusa bakin teku, sai Yesu ya ga dubban mutane suna bin su. Ko da yake Yesu da manzanninsa suna so su huta, amma ya saurari mutanen. Ya warkar da marasa lafiya da suka kawo kuma ya koyar da su. Ya wuni yana koyar da su game da Mulkin Allah. Da yamma ta yi, sai manzannin suka ce masa: ‘Mutanen suna jin yunwa. Ka sallame su don su nemi abin da za su ci.’

Yesu ya ce: ‘Bai kamata su tafi ba. Ku ba su abin da za su ci.’ Sai manzannin suka tambaye shi: ‘Kana so mu saya musu abinci?’ Amma ɗaya daga cikin manzannin mai suna Filibus ya ce: ‘Ko da mun sayi gurasa na dinari 200, ba zai ishe su ba.’

Yesu ya ce: ‘Gurasa nawa gare mu?’ Andarawus ya ce: ‘Muna da gurasa biyar da kifaye biyu. Hakika, abincin bai da yawa.’ Yesu ya ce: ‘Ku kawo gurasar da kifayen.’ Ya ce wa mutanen su raba kansu zuwa rukunin mutane 50 da 100 kuma su zauna a kan ciyawa. Sai ya ɗauki gurasar da kifayen kuma ya kalli sama ya yi addu’a. Sa’an nan Yesu ya ba manzanninsa abincin kuma suka raba wa mutanen. Dukansu maza da mata da kuma yara 5,000 sun ci sun ƙoshi. Bayan haka, manzannin sun tattara abincin da ya  rage don kada ya lalace. Raguwar ta cika kwando 12! Wannan mu’ujizar tana da ban mamaki, ko ba haka ba?

Mutanen sun yi farin ciki sosai har sun so su maida Yesu sarkinsu. Amma Yesu ya san cewa lokacin da Jehobah ya shirya ya zama sarki bai kai ba tukun. Sai ya sallami mutanen kuma ya ce wa manzanninsa su shiga jirgi zuwa tsallaken Tekun Galili. Da suka shiga cikin jirgin, sai Yesu ya haura dutse. Me ya sa? Domin yana so ya yi addu’a ga Ubansa. A ko da yaushe, Yesu yakan keɓe lokaci don ya yi addu’a ga Ubansa.

“Kada ku yi aikin neman abinci wanda yakan lalace, sai dai abinci wanda ya dawwama zuwa rai na har abada, wanda Ɗan mutum zai ba ku.”​—Yohanna 6:27