Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 61

Sun Ki Bauta wa Gunki

Sun Ki Bauta wa Gunki

Wasu ’yan shekaru bayan Sarki Nebuchadnezzar ya yi mafarki, sai ya yi wani gunki na zinariya. Ya kafa gunkin a filin da ake kira Dura kuma ya kira mutanen da suke da babban matsayi a ƙasar, har da Shadrach da Meshach da kuma Abednego don su taru a gaban gunkin. Sai sarkin ya ce: ‘Ku bauta wa wannan gunkin sa’ad da kuka ji ƙarar ƙaho da molo da kuma garaya! Za a saka duk wanda ya ƙi bauta wa gunkin cikin wuta mai zafi sosai.’ Shin waɗannan Ibraniyawa ukun za su bauta wa gunkin ne ko kuwa Jehobah ne kaɗai za su bauta wa?

Nan da nan sarkin ya ba da umurni cewa a soma kiɗa. Duk mutanen da ke wurin sun bauta wa gunkin amma Shadrach da Meshach da kuma Abednego ba su yi hakan ba. Sai wasu daga cikin mutanen suka gaya wa sarkin cewa: ‘Waɗannan Ibraniyawa ukun sun ƙi su bauta wa gunkinka.’ Sai Nebuchadnezzar ya aika a kawo su kuma ya ce: ‘Zan sake ba ku wata dama don ku bauta wa gunkin. Idan kuka ƙi, za a saka ku cikin wuta. Babu wani allahn da zai iya cece ku daga hannuna.’ Sai suka ce: ‘Ba ka bukatar ka ba mu wata dama. Allahnmu zai iya cece mu. Amma ko da bai cece mu ba, ba za mu bauta wa wannan gunkin ba, Ya sarki.’

Nebuchadnezzar ya yi fushi sosai. Sai ya gaya wa sojojinsa: ‘Ku ƙara zafin wutar har sau bakwai!’ Kuma ya umurci sojojinsa cewa: ‘Ku ɗaure waɗannan mazan kuma ku jefa su cikin wutar!’ Da sojojin suka je  kusa da wutar, sai wutar ta kashe su domin tana da zafi sosai. Ibraniyawan suka faɗi a cikin wutar. Amma da Nebuchadnezzar ya leƙa cikin wutar, sai ya ga mazaje huɗu suna yawo a cikin wutar. Hakan ya ba shi tsoro kuma ya tambayi ma’aikacin fādarsa cewa: ‘Ba mutane uku ba ne aka tura a cikin wutar ba? Amma mutane huɗu ne nake gani, kuma ɗayan ya yi kama da mala’ika!’

Nebuchadnezzar ya je kusa da wutar kuma ya ce: ‘Ku fito, ya ku bayin Allah Maɗaukaki!’ Kowa ya yi mamakin ganin Shadrach da Meshach da kuma Abednego sa’ad da suka fito daga cikin wutar ba tare da ta ƙone su ba. Fatarsu da gashinsu da kuma rigarsu ba su ƙone ba, kuma jikinsu bai yi warin hayaƙi ba.

Sai Nebuchadnezzar ya ce: ‘Allahn da Shadrach da Meshach da kuma Abednego suke bauta wa yana da iko sosai. Ya aiko da mala’ikansa ya cece su. Babu wani Allah kamar sa.’

Ka ƙuduri niyyar cewa za ka riƙe amincinka ga Jehobah ko da mene ne zai faru kamar yadda waɗannan Ibraniyawan uku suka yi?

“Ka yi sujada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta wa.”​—Matta 4:10