Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 62

Mulkin da Ke Kama da Babbar Bishiya

Mulkin da Ke Kama da Babbar Bishiya

Wata rana daddare, Nebuchadnezzar ya yi wani mafarki mai ban tsoro. Sai ya kira bayinsa masu hikima don su gaya masa ma’anar mafarkin. Amma dukansu ba su iya bayyana ma’anar mafarkin ba. A ƙarshe, sarkin ya kira Daniyel.

Nebuchadnezzar ya gaya wa Daniyel cewa: ‘Na yi mafarki kuma na ga wata bishiya. Bishiyar ta ci gaba da girma har ta kai sama. Za a iya ganin ta daga ko’ina a faɗin duniya. Tana da ganyaye masu kyau da kuma ’ya’yan itace da yawa. Dabbobi suna hutawa a inuwarta kuma tsuntsaye suna yin gida a rassanta. Sai wani mala’ika ya sauko daga sama, ya ce: “A sare itacen, a daddatse rassan. Amma a bar gindinsa a ƙasa, kuma a kewaye ta da maɗaurin ƙarfe da na jan ƙarfe. Zuciyarta za ta canja daga na mutum zuwa ta dabba, kuma za ta kasance haka har shekara bakwai. Dukan mutane za su san cewa Allah ne Maɗaukakin Sarki kuma zai iya ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.”’

Jehobah ya bayyana wa Daniyel abin da mafarkin yake nufi. Daniyel ya tsorata da ya fahimci mafarkin. Sai ya ce: ‘Ya sarki, na so da a ce wannan mafarkin game da maƙiyanka ne, amma game da kai ne. Kai ne babbar bishiyar da aka sare. Za ka rasa sarautarka kuma za ka soma cin ciyawa kamar dabba. Amma saboda mala’ikan ya ce a bar gindinsa a ƙasa, za ka sake zama sarki.’

Bayan shekara ɗaya, Nebuchadnezzar yana tafiya a saman fādarsa kuma yana kallon kyaun ƙasar Babila. Sai ya ce: ‘Duba wannan babban birnin da na gina. Hakika ni mai iko ne sosai!’ Yana cikin magana, sai murya daga sama ta ce masa: ‘Nebuchadnezzar! Daga yanzu ka rasa sarautarka.’

Nan da nan sai Nebuchadnezzar ya haukace kuma ya zama kamar dabba. Sai aka kore shi daga fādarsa kuma ya soma zama da namomin daji. Sumarsa ta yi girma kamar gashin tsuntsun da ake kira gaggafa, farcensa kuma kamar na tsuntsu.

 Nebuchadnezzar ya sami sauƙi bayan shekara bakwai kuma Jehobah ya sake naɗa shi sarkin Babila. Sai Nebuchadnezzar ya ce: ‘Ina yi wa Jehobah, Sarkin sama yabo. Yanzu na san cewa Jehobah shi ne Maɗaukakin Sarki. Yana ƙasƙantar da masu girman kai, kuma yana ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.’

“Bayan girman kai sai halaka, faɗuwa kuma tana biye da tada hanci.”​—Misalai 16:18