Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 50

Jehobah Ya Kāre Jehoshaphat

Jehobah Ya Kāre Jehoshaphat

Wani sarkin Yahuda mai suna Jehoshaphat ya halaka bagaden Baal da kuma gumaka a ƙasar. Yana so mutane su san dokokin Jehobah. Sai ya tura hakimai da Lawiyawa zuwa dukan yankunan Yahuda don su koya wa mutanen dokokin Jehobah.

Ƙasashen da ke kusa da Yahuda suna jin tsoron kai musu hari domin sun san cewa Jehobah yana tare da mutanensa. Shi ya sa suka kawo wa Sarki Jehoshaphat kyaututtuka. Amma ’yan Mowab da Ammon da kuma wasu mutane daga yankin Seir suka zo yaƙan mutanen Yahuda. Jehoshaphat ya san cewa yana bukatar taimakon Jehobah. Sai ya sa aka tara maza da mata da kuma yara a Urushalima. Ya yi addu’a a gabansu kuma ya ce: ‘Ya Jehobah, ba za mu yi nasara ba sai da taimakonka. Ka gaya mana abin da za mu yi.’

Sai Jehobah ya amsa addu’ar, ya ce: ‘Kada ku ji tsoro. Zan taimake ku. Ku tsaya shiru kuma ku ga yadda zan cece ku.’ Ta yaya Jehobah ya cece su?

Da gari ya waye, sai Jehoshaphat ya zaɓi mawaƙa, ya ce su soma tafiya kuma sojoji su bi su a baya. Sai suka taka daga Urushalima har zuwa wani filin yaƙi da ke garin Tekoa.

Yayin da mawaƙan suke rera waƙar yabo ga Jehobah da babbar murya, sai Jehobah ya ceci mutanensa. Ya rikitar da mutanen Ammon da Mowab kuma suka soma kashe junansu. Babu wanda ya tsira daga cikinsu. Amma Jehobah ya kāre mutanen Yahuda, da sojojinsu da kuma firistocinsu. Dukan mutanen da ke kusa da Yahuda sun ji labarin abin da Jehobah ya yi kuma hakan ya sa suka san cewa har ila, Jehobah yana kāre bayinsa. Ta yaya Jehobah yake ceton bayinsa? Yana amfani da hanyoyi da yawa. Ba ya bukatar taimakon mutane don ya cece su.

“Ba ku za ku yi yaƙin ba. Ku dai ku yi shirin yaƙin kawai, ku kafa kanku, ku tsaya ciki, ku ga yadda Yahweh zai yi nasara dominku.”​—2 Labarbaru 20:​17, Juyi Mai Fitar da Ma’ana