Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 99

Wani Mai Gadi Ya Zama Kirista

Wani Mai Gadi Ya Zama Kirista

Akwai wata yarinya baiwa a Filibi da take da aljani. Aljanin yana sa yarinyar ta faɗi abin da zai faru a nan gaba, kuma hakan ya sa tana samo wa masu ita kuɗi sosai. Sa’ad da Bulus da Sila suka zo Filibi, yarinyar ta yi kwanaki da yawa tana bin su. Aljanin ya sa tana ihu tana cewa: “Waɗannan mutanen bayin Allah Maɗaukaki ne.” Bulus ya ce wa aljanin: ‘A cikin sunan Yesu, ka fita daga cikin ta!’ Sai aljanin ya fita daga jikin yarinyar.

Da masu yarinyar suka ga cewa sun daina samun kuɗi daga wurinta, sai suka yi fushi sosai. Suka kai Bulus da Sila gaban hukuma kuma suka ce: ‘Waɗannan mutanen suna karya doka da kuma jawo tashin hankali a cikin gari!’ Sai hukuma ta ce a yi wa Bulus da Sila bulala kuma a saka su cikin kurkuku. Mai kula da kurkukun ya saka su a cikin wani ɗaki mai duhu sosai kuma ya ɗaura musu hannu da ƙafa.

Bulus da Sila sun rera waƙoƙin yabo ga Jehobah kuma sauran fursunonin suna jin su. Sai da tsakar dare, aka yi wata girgizar ƙasa da ta girgiza kurkukun sosai. Ƙofofin kurkukun sun buɗe kuma ɗaurin da aka yi musu ya kwance. Mai kula da kurkukun ya shiga cikin kurkukun kuma ya ga ƙofofin a buɗe. Sai ya ɗauka cewa duka fursunonin sun gudu. Don haka, ya ɗauki wuƙa yana so ya kashe kansa.

Nan da nan, sai Bulus ya ce: ‘Kada ka kashe kanka! Dukanmu muna nan!’ Mai kula da kurkukun ya zo wurinsu a guje. Ya ɗurkusa a gaban Bulus da Sila ya ce: “Me zan yi don in sami ceto?” Sai suka ce masa: ‘Kai da iyalinka kuna bukatar ku yi imani da Yesu.’ Bulus da Sila sun koya musu kalmar Jehobah kuma mai kula da kurkukun da iyalinsa suka yi baftisma.

“Za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami’u da kurkuku, su kuma kai ku gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana. Wannan zai zamar muku hanyar ba da shaida.”​—Luka 21:​12, 13, Littafi Mai Tsarki