Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 1

Gabatarwar Sashe na 1

Labarin yadda Allah ya halicci abubuwa masu kyau a sama da kuma ƙasa ne aka fara ba da a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan kana da yara, ka taimaka musu su ga abubuwan ban al’ajabi da aka halitta. Ka ambata yadda ’yan Adam suka yi dabam da dabbobi, domin Allah ya halicce su da ikon yin magana da tunani da ƙera abubuwa da yin waƙa da kuma addu’a. Ka sa yaranka su nuna godiya don ikon Jehobah da hikimarsa da kuma ƙaunarsa ga dukan halittunsa.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 1

Allah Ya Yi Sama da Duniya

Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya yi sama da duniya. Amma ka san mala’ikan da ya fara halitta kafin ya yi sauran abubuwa?

DARASI NA 2

Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko

Allah ya yi mace da miji na farko kuma ya saka su a lambun Adnin. Za su iya haifan ’ya’ya kuma su mai da duniya gabaki daya aljanna.