Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 2

Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko

Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko

Jehobah ya yi lambu a wani wuri da ake kira Adnin. Akwai fulawoyi da itatuwa da kuma dabbobi dabam-dabam a lambun. Bayan haka, sai Allah ya halicci mutum na farko mai suna Adamu da ƙasa. Sai ya hura iska a hancinsa. Ka san abin da ya faru bayan haka? Mutumin ya soma numfashi! Sai Jehobah ya gaya wa Adamu cewa ya kula da lambun kuma ya ba dukan dabbobin da ke wurin suna.

Allah ya ba Adamu wata doka. Ya ce: ‘Za ka iya ci daga dukan itatuwan da ke lambun amma ban da guda ɗaya. A ranar da ka ci ’ya’yan itacen nan, za ka mutu.’

Bayan haka, sai Jehobah ya ce: ‘Zan yi ma Adamu macen da za ta riƙa taimaka masa.’ Allah ya sa Adamu ya yi barci sosai, sai ya cire ƙashin da ke ƙirjinsa ya yi macen da shi. Sunanta Hauwa’u. Adamu da Hauwa’u su ne iyali na farko a duniya. Yaya Adamu ya ji  sa’ad da Allah ya ba shi mata? Ya yi farin ciki sosai kuma ya ce: ‘Duba abin da Jehobah ya yi da ƙashin ƙirjina! Abin mamaki! An yi wata kamar ni.’

Sai Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u cewa su haifi yara kuma su cika duniya. Yana so su yi aiki tare don su mai da duniya Aljanna, wato wuri mai kyau kamar lambun Adnin kuma yana so su ji daɗin aikin da ya ba su. Amma hakan bai faru ba. Me ya sa? Za mu san dalilin a babi na gaba.

‘Shi wanda ya yi su tun farko, namiji da mace ya yi su.ʼ​—Matta 19:4