Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 59

Matasa Hudu da Suka Yi wa Jehobah Biyayya

Matasa Hudu da Suka Yi wa Jehobah Biyayya

Sa’ad da Nebuchadnezzar ya kai hakiman Yahuda ƙasar Babila, ya sa Ashpenaz wanda shi ma’aikaci ne a fādar ya riƙa kula da su. Sarki Nebuchadnezzar ya gaya wa Ashpenaz cewa ya zaɓo samari masu ƙoshin lafiya da kuma hikima sosai a cikinsu. Za a horar da su har shekara uku. Wannan horarwar za ta taimaka musu su zama ma’aikata a Babila. Ana so matasan su koyi karatun Babila da rubutunsu da kuma yarensu. Ana kuma so su ci irin abincin da sarki da kuma waɗanda suke fādar suke ci. Sunayen huɗu daga cikin waɗannan matasan su ne Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya. Ashpenaz ya ba su sunan mutanen Babila, wato Belteshazzar da Shadrach da Meshach da kuma Abednego.  Abubuwan da aka koya musu za su sa su daina bauta wa Jehobah kuwa?

Waɗannan matasan sun ƙuduri niyyar cewa za su yi wa Jehobah biyayya. Sun san cewa bai kamata su ci abincin sarkin ba domin Dokar Allah ta haramta cin wasu daga cikin abincin. Hakan ya sa suka gaya wa Ashpenaz cewa: ‘Don Allah kada ka sa mu mu ci abincin sarki.’ Sai Ashpenaz ya ce: ‘Sarki zai kashe ni idan kuka ƙi cin abincin kuma ya ga cewa ba ku da ƙoshin lafiya!’

Daniyel ya yi wani tunani. Sai ya gaya wa mai kula da su cewa: ‘Don Allah, ka ba mu kayan lambu da kuma ruwa kawai har kwana goma. Bayan haka, ka gwada mu da sauran mazan da suka ci abincin sarkin.’ Sai mai kula da su ya amince da hakan.

Bayan kwana goma, Daniyel da abokansa uku sun fi sauran mazan ƙoshin lafiya. Jehobah ya yi farin ciki sosai don sun yi masa biyayya. Har ma ya ba Daniyel basirar fahimtar wahayoyi da kuma mafarkai.

Da aka gama horar da su, sai Ashpenaz ya kawo su wurin Nebuchadnezzar. Sarkin ya yi magana da su kuma ya ga cewa Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya sun fi sauran mazan ilimi da ƙwazo. Sai ya zaɓe su su yi aiki a fādarsa. Sarkin yakan nemi shawararsu a kan wasu batutuwa masu muhimmanci. Jehobah ya ba su hikima fiye da sauran mutane masu hikima a ƙasar.

Ko da yake suna wata ƙasa dabam, Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya ba su manta cewa su mutanen Jehobah ba ne. Shin za ka ci gaba da bauta wa Jehobah ko a lokacin da iyayenka ba sa tare da kai?

“Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.” ​—⁠Misalai 27:⁠11