Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 65

Esther Ta Ceci Mutanenta

Esther Ta Ceci Mutanenta

Esther Bayahudiya ce da take zama a birnin Shushan a ƙasar Fasiya. Shekaru da yawa da suka shige, Nebuchadnezzar ya kwashe danginta daga Urushalima zuwa zaman bauta a ƙasarsa. Don haka, kawunta mai suna Mordekai ya yi renonta kuma shi bawan Sarkin Fasiya ne mai suna Ahasuerus.

Sarki Ahasuerus yana bukatar sarauniya. Sai bayinsa suka kawo masa kyawawan matan da ke ƙasar har da Esther. Amma a cikinsu duka, Esther ce sarkin ya zaɓa ta zama sarauniyarsa. Mordekai ya gaya wa Esther cewa kada ta gaya wa kowa ita Bayahudiya ce.

Haman shi ne shugaban dukan hakimai kuma yana da fahariya sosai. Yana so kowa ya riƙa bauta masa. Amma Mordekai ya ƙi kuma hakan ya sa Haman fushi sosai kuma ya so ya kashe shi. Da aka gaya wa Haman cewa Mordekai Bayahude ne, sai ya yi tunanin yadda zai iya sa a kashe dukan Yahudawa a ƙasar. Ya gaya wa sarkin cewa: ‘Waɗannan Yahudawan mugayen mutane ne sosai. Don haka a kashe su.’ Sai Ahasuerus ya ce: ‘Ka je ka yi duk abin da kake so ka yi.’ Kuma ya ba wa Haman ikon kafa doka. Haman ya kafa wata doka da ta ba mutanen dama su kashe dukan Yahudawa a ranar 13 ga watan Adar. Jehobah yana ganin abin da ke faruwa.

Esther ba ta san da dokar ba. Don haka, Mordekai ya aika mata takardar dokar kuma ya ce mata: ‘Ki je ki yi magana da sarkin.’ Sai Esther ta ce: ‘Za a kashe duk wanda ya je wurin sarkin ba tare da an gayyace shi ba. Yanzu kwana 30 ke nan da ban je wurin sarki ba! Amma zan je wurinsa. Zan rayu idan ya miƙa sandar sarautarsa. Idan bai yi hakan ba, za a kashe ni.’

Sai Esther ta je fādar sarkin. Da sarkin ya gan ta, sai ya miƙa sandarsa. Sai ta je wurinsa kuma ya ce mata: ‘Me kike so  Esther?’ Sai ta ce: ‘Ina so na gayyace ka da Haman zuwa liyafar da na shirya yau.’ A wurin liyafar, sai Esther ta ƙara gayyatar su zuwa wata liyafa kuma. Da suka sake zuwa, sai sarkin ya ƙara tambayar ta cewa: ‘Me kike so?’ Sai ta ce: ‘Wani yana so ya kashe ni da kuma mutanena. Don Allah ka taimaka mana.’ Sai sarkin ya ce: ‘Wane ne yake so ya kashe ki?’ Sai ta ce: ‘Mugun mutumin shi ne Haman.’ Hakan ya sa Ahasuerus fushi sosai kuma nan da nan ya ce a kashe Haman.

Amma babu wani da zai iya soke dokar da Haman ya kafa, ko sarkin da kansa. Don haka, sarkin ya naɗa Mordekai shugaban hakimai kuma ya ba shi ikon ya sake kafa sabuwar doka. Sai Mordekai ya kafa dokar da ta ba Yahudawa ’yanci su kāre kansu sa’ad da mutanen suka kawo musu hari. A ranar 13 ga watan Adar, Yahudawan sun ci nasara a kan maƙiyansu. Tun daga ranar, suna yin biki kowace shekara don su tuna da wannan nasarar da suka yi.

‘A gaban mahukunta da sarakuna za a kawo ku saboda ni, domin shaida garesu da al’ummai kuma.’​—Matta 10:18