Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 14

Gabatarwar Sashe na 14

Kiristoci a ƙarni na farko sun yaɗa bishara game da Mulki a wurare da yawa. Yesu ya nuna musu wurin da za su yi wa’azi kuma ya taimaka musu su iya yi wa mutane wa’azi a yarensu. Jehobah ya sa sun kasance da gaba gaɗi kuma ya ba su ƙarfi su jimre duk tsanantawar da aka yi musu.

Yesu ya saukar wa manzo Yohanna da wahayi da ya nuna ɗaukakar Allah. A wani wahayi, manzon ya ga yadda Mulkin Allah ya halaka Shaiɗan da kuma mabiyansa har abada. Ya ga Yesu da kuma mutane 144,000 suna sarauta. Ƙari ga haka, Yohanna ya ga duniya ta zama aljanna, mutane suna zaman lafiya kuma suna bauta wa Jehobah cikin haɗin kai.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 94

An Ba Mabiyan Yesu Ruhu Mai Tsarki

Wani abu ne ruhu mai tsarkin ya taimaka musu su yi?

DARASI NA 95

Sun Ki Su Daina Wa’azi

Malaman addinai da suka sa aka kashe Yesu suna son su hana mabiyansa yin wa’azi. Amma ba za su iya ba.

DARASI NA 96

Yesu Ya Zabi Shawulu

Bulus ya tsani Kiristoci, amma ra’ayinsa ya kusan canjawa.

DARASI NA 97

Karniliyus Ya Sami Ruhu Mai Tsarki

Me ya sa Allah ya aika Bitrus zuwa gidan wannan mutumin da ba Bayahude ba?

DARASI NA 98

Mutane da Yawa Sun Zama Kiristoci

Manzo Bulus da abokansa sun soma wa’azi a kasashe masu nisa.

DARASI NA 99

Wani Mai Gadi Ya Zama Kirista

Ta yaya aljani da girgizar kasa da kuma takobi suka shafi wannan labarin?

DARASI NA 100

Bulus da Timotawus

Su biyu sun yi shekaru da yawa suna aiki tare

DARASI NA 101

An Tura Bulus Kasar Roma

Tafiyar da suka yi na cike da hatsari, amma babu abin da ya isa ya hana wannan manzon yin hidimarsa.

DARASI NA 102

Wahayin da Aka Saukar wa Yohanna

Yesu ya saukar masa da wahayoyi game da nan gaba.

DARASI NA 103

Bari “Mulkinka Ya Zo”

Wahayin da Yohanna ya gani ya nuna yadda Mulkin Allah zai canja yanayinmu a duniya.