Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 21

Annoba ta Goma

Annoba ta Goma

Musa ya yi wa Fir’auna alkawari cewa ba zai sake zuwa wurinsa ba. Amma kafin ya tafi, ya gaya masa cewa: ‘Kowane ɗan fari na ʼyan Masar zai mutu da daren nan har da ɗan Fir’auna ma.’

Sai Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su dafa wani irin abinci. Ya ce: ‘Ku yanka bunsuru ko rago mai shekara ɗaya kuma ku yafa jininsa a ƙofarku. Ku gasa naman kuma ku ci da burodin da ba a saka masa yisti ba. Ku saka riga da kuma takalmi kuma ku kasance da shiri don za ku tafi da daren nan.’ Babu shakka, Isra’ilawa sun yi murna sosai, ko ba haka ba?

Mala’ikan Jehobah ya shiga duka gidajen Masarawa da tsakar dare. Duk gidan da ba su yafa jini a ƙofarsu ba, ɗan farinsu ya rasu. Amma mala’ikan bai shiga gidajen da aka yafa jini a ƙofarsu ba. ʼYan farin Masarawa masu arziki da talakawa duk sun mutu. Amma babu ko ɗaya cikin ’ya’yan Isra’ilawa da ya mutu.

Yaron Fir’auna ma ya mutu. Nan da nan, sai Fir’auna ya gaya wa Musa da Haruna cewa: ‘Ku tashi, ku fita daga ƙasar nan. Ku tafi ku bauta wa Allahnku. Ku tafi da dukan dabbobinku!’

An shirya Isra’ilawa bisa iyali da ƙabila kuma sun fita daga ƙasar Masar ana farin wata. Akwai Isra’ilawa maza  600,000 da mata da kuma yara da yawa. Har ila, mutane da yawa da ba Isra’ilawa ba sun bi su don su bauta wa Jehobah. Yanzu, Isra’ilawa sun samu ’yanci!

A kowace shekara, Isra’ilawa suna yin biki don su riƙa tunawa da yadda Jehobah ya cece su. Ana kiran wannan bikin Idin Ƙetarewa.

“Na tashe ka ka zama sarki da nufi cewa in nuna ikona ta wurinka, a kuma sanar da sunana cikin duniya duka.”​—Romawa 9:​17, Juyi Mai Fitar da Ma’ana