Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 6

Mutane Takwas Sun Tsira

Mutane Takwas Sun Tsira

Nuhu da iyalinsa da kuma dabbobi ne suka shiga cikin jirgin. Jehobah ya rufe ƙofar kuma aka soma ruwan sama. An yi ta ruwa sosai amma jirgin bai nitse ba. Sai ruwan ya rufe duniya gabaki ɗaya. Dukan mugayen mutanen sun mutu. Amma Nuhu da iyalinsa sun tsira. Babu shakka sun yi farin ciki don sun yi biyayya ga Jehobah, ko ba haka ba?

An yi kwana 40, dare da rana ana ruwan sama. Bayan haka, sai ruwan ya tsaya. A hankali a hankali, ruwan ya soma bushewa. A ƙarshe, sai jirgin ya sauka a kan dutse. Amma Nuhu da iyalinsa ba su fita daga jirgin ba tukun domin ruwan bai gama bushewa ba.

A hankali a hankali, sai ruwan ya bushe. Nuhu da iyalinsa sun yi fiye da shekara ɗaya a cikin jirgin. Sai Jehobah ya gaya musu su fita daga jirgin don su zauna a duniyar da babu mugayen mutane a ciki. Sun gode wa Jehobah sosai don ba su mutu ba kuma sun miƙa masa hadaya.

Jehobah ya yi farin ciki don hadayar da suka yi. Sai ya ce ba zai sake yin amfani da ruwa wajen halaka duniya ba. Don ya nuna cewa ba zai sake yin haka ba, sai ya sa rambo, wato bakan gizo na farko ya fito. Ka taɓa ganin bakan gizo?

Bayan haka, sai Jehobah ya gaya wa Nuhu da iyalinsa cewa su haifi yara kuma su cika duniya.

“Nuhu ya shiga jirgin. Kafin [mutanen] su san abin da ake ciki, babbar ambaliyar ruwa ta zo ta kwashe su duka.”​—Matta 24:​38, 39, Juyi Mai Fitar da Ma’ana