Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 37

Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila

Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila

Eli Babban Firist yana da yara biyu da suke hidimar firist a mazauni. Sunayensu Hophni da Finehas ne. Ba su yi biyayya ga Jehobah ba kuma suna ba mutane wahala. Idan mutane suka kawo hadaya ga Jehobah, sai Hophni da Finehas su ɗauki nama mai soka su ci. An gaya wa Eli abin da yaransa suke yi amma bai yi musu kome ba. Shin Jehobah zai bar su su riƙa yin haka ne?

Ko da yake Hophni da Finehas sun girme Sama’ila, amma bai koyi halinsu ba. Abin da Sama’ila ya yi ya sa Jehobah farin ciki sosai. Wata rana da yake barci da dare, sai ya ji wani yana kiransa. Ya tashi da gudu ya je wurin Eli ya ce: ‘Ga ni!’ Amma Eli ya ce masa: ‘Ban kira ka ba. Ka koma ka yi barci.’ Sai Sama’ila ya koma ya kwanta. Sai aka sake kiransa. Da hakan ya faru sau uku, sai Eli ya gane cewa Jehobah ne yake kiran Sama’ila. Sai Eli ya gaya wa Sama’ila cewa idan ya sake jin kiran, ya ce: ‘Jehobah, ka yi magana bawanka yana sauraro.’

Da Sama’ila ya koma ya kwanta, sai ya ji ana cewa: ‘Sama’ila, Sama’ila!’ Sai ya ce: ‘Ka yi magana, bawanka yana sauraro.’ Sai Jehobah ya ce masa: ‘Ka gaya wa Eli cewa zan yi wa shi da  iyalinsa horo. Ya san cewa yaransa suna yin abubuwa marasa kyau a mazauni, amma bai yi musu kome ba.’ Da safe ya yi, sai Sama’ila ya buɗe ƙofofin mazaunin kamar yadda ya saba. Amma yana jin tsoro ya gaya wa Eli abin da Jehobah ya gaya masa. Sai Eli ya kirawo shi ya ce: ‘Ɗana, mene ne Jehobah ya gaya maka? Kar ka ɓoye mini kome.’ Sai Sama’ila ya gaya wa Eli kome da kome.

Jehobah ya ci gaba da kula da Sama’ila yayin da yake girma. Duk mutanen ƙasar sun san cewa Jehobah ne ya zaɓi Sama’ila ya zama annabi da kuma alƙali.

“Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.”​—Mai-Wa’azi 12:1