Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 79

Yesu Ya Yi Mu’ujizai da Yawa

Yesu Ya Yi Mu’ujizai da Yawa

Yesu ya zo duniya don ya yi wa’azi game da Mulkin Allah. Jehobah ya ba Yesu ikon yin mu’ujizai don ya nuna abin da zai yi idan ya zama Sarki. Yana warkar da kowace irin cuta. Marasa lafiya sun bi shi duk inda ya je don neman taimako kuma ya warkar da su duka. Ya warkar da makafi da kurame da masu cutar shanyewar jiki da kuma waɗanda aljanu suka shiga jikinsu. Marasa lafiya suna warkewa ko da rigar Yesu kawai suka taɓa. Mutane sun bi Yesu a duk inda ya tafi. Kuma yana taimaka musu ko da a lokacin da yake so ya huta.

Wata rana da Yesu yake wani gida, sai mutane suka kawo wani mutum da ke da cutar shanyewar jiki. Amma ba su iya shiga ba domin gidan yana cike da mutane. Don haka suka yi wani rami a saman gidan kuma suka sauko da mutumin daidai kusa da Yesu. Sai Yesu ya ce wa mutumin: ‘Ka tashi ka yi tafiya.’ Mutane sun yi mamaki da suka ga mutumin ya tashi ya yi tafiya.

Wata rana, wasu kutare guda goma sun ga Yesu sa’ad da yake zuwa wani ƙauye, sai suka yi ihu suka ce: ‘Yesu, ka taimake mu!’ A dā, ba a barin kutare su zo kusa da mutane. Sai Yesu ya ce musu su je haikali kamar yadda Dokar Jehobah ta umurci kutare su yi bayan sun warke. Suna cikin tafiya zuwa haikalin, sai suka warke. Sa’ad da ɗaya daga cikin kutaren ya ga cewa ya warke, sai ya koma ya yi wa Yesu godiya kuma ya  ɗaukaka Allah. A cikin kutaren duka, guda ɗaya ne kawai ya koma ya gode wa Yesu.

Wata mata da ta yi shekara 12 tana rashin lafiya tana so ta warke. Sai ta bi cikin mutane kuma ta taɓa rigar Yesu. Nan da nan sai ta warke. Sa’ad da hakan ya faru, sai Yesu ya ce: “Wane ne ya taɓa ni?” Hakan ya sa matar ta tsorata kuma ta zo wurinsa ta gaya masa gaskiyar al’amarin. Yesu ya ƙarfafa, ya ce: ‘’Yata, ki sauka lafiya.’

Wani ma’aikaci mai suna Yariyus ya roƙi Yesu cewa: ‘Ka zo gidana! ’Yata ba ta da lafiya.’ Amma yarinyar ta mutu kafin Yesu ya kai gidan Yariyus. Da Yesu ya zo, ya ga mutane da yawa sun zo don su yi wa iyalin ta’aziya. Yesu ya ce musu: ‘Ku daina kuka, barci take yi.’ Sai ya riƙe hannun yarinyar kuma ya ce: “Yarinya ki tashi!” Nan da nan yarinyar ta tashi kuma Yesu ya gaya wa iyayenta su ba ta abinci. Ka yi tunanin irin farin cikin da iyayen suka yi!

“Allah ya zuba masa ruhu mai-tsarki da iko: ya yi yawo yana aikin alheri, yana warkar da dukan waɗanda Shaitan ke wahal da su; gama Allah yana tare da shi.”​—Ayyukan Manzanni 10:⁠38