Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 25

Mazauni don Ibada

Mazauni don Ibada

A lokacin da Musa yake Dutsen Sinai, Jehobah ya gaya masa ya gina wani tanti da ake kira mazauni. Isra’ilawa za su riƙa bauta masa a wurin. Kuma za su iya ɗaukan wannan mazaunin zuwa duk inda za su je.

Sai Jehobah ya ce: ‘Ka gaya wa mutanen su yi gudummawa iya ƙarfinsu don a gina mazauni da shi.’ Sai Isra’ilawan suka ba da zinariya da azurfa da jan ƙarfe da wasu irin duwatsu masu tsada da kuma kayan ado. Ban da haka ma, sun ba da yadi da auduga da fata da kuma wasu abubuwa da yawa. Abubuwan sun yi yawa sosai har Musa ya gaya musu: ‘Gudummawar ta yi yawa! Ku daina kawowa.’

Maza da mata da yawa da suka iya gini sun taimaka wajen gina mazaunin. Jehobah ya ba su hikima don su yi aikin. Wasu sun yi saƙar zare da kuma yadi. Wasu kuma sun jera duwatsu, sun yi wa mazaunin ado da gwal ko itace.

Mutanen sun gina mazaunin yadda Jehobah ya gaya musu. Sun yi wani labulen da ya raba mazaunin biyu, wato wuri Mai Tsarki da wuri Mafi Tsarki. Akwai akwatin alkawari a wuri Mafi Tsarkin. An yi akwatin da itace da kuma gwal. Akwai fitila na gwal da teburi da bagadi na ƙona turare a wuri Mai Tsarkin. A cikin farfajiya akwai kwanon jan ƙarfe da kuma babban bagadi. Akwatin alkawarin ya tuna wa Isra’ilawa alkawarin da suka yi na yin biyayya ga Jehobah.

 Jehobah ya zaɓi Haruna da yaransa su zama firist a mazaunin. Za su riƙa yin hidima da kuma hadaya ga Jehobah. Haruna babban firist ne kaɗai yake da izinin shiga wuri Mafi Tsarki. Yana shiga wurin sau ɗaya a shekara don yin hadaya saboda zunubansa da na iyalinsa da na dukan Isra’ilawa.

Isra’ilawan sun gama gina mazaunin shekara ɗaya bayan da suka bar ƙasar Masar. Yanzu sun sami wurin da za su riƙa bauta wa Jehobah.

Jehobah ya cika wurin da ɗaukakarsa kuma gajimare ya sauka a kan mazaunin. Idan Isra’ilawa suka ga gajimare a kan mazaunin, sai su ci gaba da zama. Amma idan suka ga gajimaren ya soma tafiya, sun san cewa lokacin tafiya ya yi. Sai su ɗauki mazaunin kuma su bi gajimaren.

“Na ji babbar murya kuwa daga cikin kursiyin, ta ce, duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su.”​—Ru’ya ta Yohanna 21:3