Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 75

Shaidan Ya Jarraba Yesu

Shaidan Ya Jarraba Yesu

Bayan da Yesu ya yi baftisma, sai ruhu mai tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji. Yesu ya ji yunwa sosai domin ya yi azumi na kwana 40. Bayan haka, sai Shaiɗan ya zo ya jarraba Yesu kuma ya ce: ‘Idan da gaske kai Ɗan Allah ne, ka juya dutsen nan zuwa burodi.’ Amma Yesu ya faɗi abin da Nassosi suka ce: ‘An rubuta cewa ba abinci ne kaɗai zai sa mu rayu ba. Amma ya kamata mu yi biyayya ga umurnin Jehobah.’

Bayan haka, sai Shaiɗan ya ce wa Yesu: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, ka faɗo daga saman haikalin. Domin an rubuta cewa Allah zai aiko da mala’ikunsa su riƙe ka.’ Amma Yesu ya sake faɗin abin da ke cikin Nassosi: ‘An rubuta cewa kada mu gwada Jehobah.’

Sai Shaiɗan ya sake nuna wa Yesu dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu da kuma wadatarsu. Ya ce: ‘Zan ba ka duka waɗannan mulkokin da kuma ɗaukakarsu idan ka bauta mini sau ɗaya kawai.’ Sai Yesu ya ce masa: ‘Ka rabu da ni Shaiɗan! Domin an rubuta cewa ya kamata mu bauta wa Jehobah kaɗai.’

Sai Shaiɗan ya rabu da shi kuma mala’iku suka zo suka ba Yesu abinci. Daga lokacin, sai Yesu ya soma yin wa’azin Mulkin Allah. Wannan shi ne aikin da aka aiko shi ya yi a duniya. Mutane sun so koyarwa Yesu kuma suna bin sa duk inda ya je.

“Sa’ad da [Shaiɗan] yake yin ƙarya, don kansa yake yi: gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.”​—Yohanna 8:44