Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 12

Yakubu Ya Sami Gādo

Yakubu Ya Sami Gādo

Ishaƙu yana da shekara 40 sa’ad da ya auri Rifkatu kuma yana son ta sosai. Bayan wani lokaci, sai suka haifi ʼyan biyu, maza.

Sunan babban Isuwa ne, na biyun kuma Yakubu. Isuwa yana son zuwa yawo kuma ya iya farauta sosai. Amma Yakubu yana son zama a gida.

A lokacin, idan mahaifin wani ya mutu, ana ba ɗan fari yawanci filaye da kuɗin mahaifinsa. Ana kiran hakan gādo. A iyalin Ishaƙu kuma, gādon ya haɗa da alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim. Isuwa bai damu sosai da waɗannan alkawuran ba, amma Yakubu ya ɗauke su da muhimmanci.

Wata rana, sai Isuwa ya dawo gida daga farauta a gajiye. Da ya ji ƙamshin abincin da Yakubu yake dafawa, sai ya ce: ‘Ina jin yunwa sosai! Ka ɗiba mini jar miyarka!’ Sai Yakubu ya ce: ‘Zan ba ka idan ka sayar mini da gādonka na haihuwa.’ Isuwa ya ce: ‘Ban damu da gādona ba! Na sayar maka, ni dai ka ba ni abinci.’ Shin abin da Isuwa ya yi yana da kyau kuwa? A’a. Isuwa ya sayar da wani abu mai muhimmanci saboda jar miya kawai.

Yanzu Ishaƙu ya tsufa kuma lokaci ya yi da ya kamata ya albarkaci ɗansa na fari. Amma Rifkatu ta sa Yakubu, ƙanen Isuwa ya sami albarkar. A lokacin da Isuwa ya gane abin da ya faru, ya yi fushi sosai kuma ya yi ƙoƙari ya kashe Yakubu. Da yake Ishaƙu da Rifkatu ba  sa son wani abu ya sami Yakubu, sai suka ce masa: ‘Yanzu fa ka gudu zuwa wurin Laban ɗan’uwan mamarka har sai ɗan’uwanka ya daina fushi.’ Yakubu ya bi shawarar da iyayensa suka ba shi kuma ya gudu don kada a kashe shi.

“Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?”​—Markus 8:​36, 37, Littafi Mai Tsarki