Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 100

Bulus da Timotawus

Bulus da Timotawus

Timotawus wani matashi ne a ikilisiyar Listra. Babansa ɗan Girka ne, mamarsa kuma Bayahudiya ce. Mamarsa Afiniki da kakarsa Lois sun koya masa game da Jehobah tun yana ƙarami.

Sa’ad da Bulus ya sake zuwa Listra, ya lura cewa Timotawus yana ƙaunar ’yan’uwa a ikilisiya sosai kuma yana so ya taimaka musu. Sai Bulus ya ce Timotawus ya zama abokin wa’azinsa. Da shigewar lokaci, Bulus ya koya masa yin wa’azi da koyarwa kuma ya ƙware sosai.

Ruhu mai tsarki ya yi wa Bulus da Timotawus ja-goranci a duk inda suka je. Wata rana daddare, sai Bulus ya ga wahayi. Wani mutum a wahayin ya gaya masa cewa ya zo Makidoniya ya taimaka musu. Sai Bulus da Timotawus da Sila da kuma Luka suka je wa’azi a wurin kuma suka kafa sababbin ikilisiyoyi.

Mutane da yawa sun zama Kiristoci a birnin Tasalonika a Makidoniya. Amma sai wasu Yahudawa suka soma kishin Bulus da abokansa. Suka soma tawaye kuma suka kai ʼyan’uwan wurin hukumomin birnin. Suka ce: ‘Mutanen nan ba sa son sarkin Roma!’ Sai Bulus da Timotawus suka gudu zuwa Biriya daddare don kada a kashe su.

Yahudawa da ʼyan Girka da ke Biriya sun saurare su kuma sun zama Kiristoci. Amma sa’ad da wasu Yahudawa daga Tasalonika suka zo garin suna tawaye, sai Bulus ya koma birnin Atina. Timotawus da Sila suka zauna a Biriya don su ƙarfafa ʼyan’uwan. Daga baya, sai Bulus ya ce Timotawus ya koma Tasalonika don ya taimaka wa ʼyan’uwa da ke fuskantar tsanantawa. Bayan  wani lokaci, Bulus ya ce Timotawus ya je ya ƙarfafa wasu ikilisiyoyi da yawa.

Bulus ya ce wa Timotawus: ‘Dole ne a tsananta wa bayin Jehobah.’ An tsananta wa Timotawus kuma an saka shi cikin kurkuku domin shi Kirista ne. Ya yi farin ciki don zarafin da yake da shi na riƙe aminci ga Jehobah.

Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Filibi cewa: ‘Zan aika muku Timotawus. Zai koya muku yadda za ku bauta wa Allah, kuma zai koya muku yin wa’azi.’ Bulus ya yarda da Timotawus. Sun yi shekaru da yawa suna hidima tare kuma sun zama abokai.

“Ba ni da wani kamarsa wanda ya damu da ku sosai. Sauran dai, abin da ya shafe kansu ne kawai sun damu da shi, ba abin da ya shafi Yesu Almasihu ba.”​—Filibiyawa 2:​20, 21, Juyi Mai Fitar da Ma’ana