Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwar Sashe na 8

Gabatarwar Sashe na 8

Jehobah ya albarkaci Sulemanu kuma ya ba shi hikima da kuma damar gina haikalin. Amma daga baya ya daina bauta wa Jehobah. Idan kana da yara, ka bayyana musu yadda bauta ta ƙarya ta sa Sulemanu ya daina bauta wa Allah. An raba mulkin kuma wasu sarakuna su sa mutanen suka soma bautar gumaka. A wannan lokacin, an kashe annabawan Jehobah masu aminci da yawa. Sarauniya Jezebel ta sa mutanen da ke arewacin ƙasar bautar gumaka. A lokacin, Isra’ilawa ba sa bauta wa Jehobah. Amma da akwai wasu amintattun bayin Jehobah kamar su Sarki Jehoshaphat da kuma annabi Iliya.

A WANNAN SASHEN

DARASI NA 44

Haikalin Jehobah

Allah ya amince da addu’ar Sarki Sulemanu kuma ya albarkace shi sosai.

DARASI NA 45

An Raba Mulkin

Isra’ilawa da yawa sun daina bauta wa Jehobah.

DARASI NA 46

Jehobah Ne Allah Na Gaskiya

Wane ne Allah Na Gaskiya? Jehobah ko Baal?

DARASI NA 47

Jehobah Ya Karfafa Iliya

Shin Jehobah zai iya karfafa ka?

DARASI NA 48

Yaron Wata Gwauruwa Ya Tashi Daga Mutuwa

An yi mu’ujiza guda biyu a wani gida!

DARASI NA 49

An Hukunta Wata Muguwar Sarauniya

Jezebel ta yi shiri a kashe wani dan Isra’ila mai suna Naboth don ta kwace gonarsa! Amma Jehobah ya ga kulle-kullen da ta yi kuma ya hukunta ta.

DARASI NA 50

Jehobah Ya Kāre Jehoshaphat

Sa’ad da makiya suke so su kai wa Yahuda hari, sarki Jehoshaphat ya roki taimakon Allah.