Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 32

Sabon Shugaba da Mata Biyu Masu Karfin Zuciya

Sabon Shugaba da Mata Biyu Masu Karfin Zuciya

Joshua ya mutu yana da shekara 110. Ya mutu bayan da ya yi shekaru da yawa yana wa mutanen Jehobah ja-goranci. Isra’ilawa sun bauta wa Jehobah a lokacin da Joshua yake musu ja-goranci. Amma bayan da Joshua ya mutu, sai suka soma bauta wa wasu alloli kamar yadda Kan’aniyawa suke yi. Da yake sun ƙi yin biyayya, sai Jehobah ya ƙyale sarkin Kan’ana mai suna Jabin ya riƙa ba su wahala. Mutanen sun roƙi Jehobah ya taimake su. Sai Jehobah ya naɗa musu sabon shugaba mai suna Barak. Shugaban zai sa mutanen su riƙa bauta wa Jehobah.

Sai wata annabiya mai suna Deborah ta aika a kirawo Barak. Jehobah ya ce ta gaya masa cewa: ‘Ka ɗauki maza 10,000 kuma ku je wurin sojojin Jabin a Kogin Kishon. Za ka ci Sisera shugaban sojojin Jabin da yaƙi.’ Sai Barak ya ce wa Deborah: ‘Idan za ki bi mu, zan je.’ Sai ta ce: ‘Zan je tare da ku. Amma Jehobah ya ce ba kai ne za ka kashe Sisera ba, mace ce za ta kashe shi.’

Sai Deborah ta tafi tare da Barak da sojojinsa zuwa Dutsen Tabor don su yi shirin yaƙi. Da Sisera ya ji hakan, sai ya tattara  karusan yaƙinsa da sojojinsa a kwarin da aka nuna a hoton nan. Sai Deborah ta ce wa Barak: ‘Yau Jehobah zai sa ka yi nasara.’ Sai Barak da maza 10,000 suka haura dutsen don su yi yaƙi da Sisera da sojojinsa.

Jehobah ya sa Kogin Kishon ya cika da ruwa. Kuma karusan yaƙin Sisera suka kafe a cikin lakar. Sai Sisera ya fita daga cikin karusarsa kuma ya soma guduwa. Barak da sojojinsa suka ci sojojin Sisera da yaƙi amma shi Sisera ya gudu! Sai ya je ya ɓoye a gidan wata mata mai suna Jael. Sai Jael ta ba shi madara ya sha kuma ta rufe shi da bargo. Da yake ya gaji sosai sai ya yi barci. Sai Jael ta nufi wajensa a hankali ta kafa ƙusa a kansa. Sai ya mutu.

Da Barak ya zo neman Sisera sai Jael ta fita daga tantin ta ce masa: ‘Mu je ciki, zan nuna maka mutumin da kake nema.’ Da Barak ya shiga, sai ya ga Sisera can kwance, ya mutu. Sai Barak da Deborah suka yi waƙa suna yabon Jehobah don yadda ya sa Isra’ilawa suka ci magabtansu da yaƙi. Hakan ya sa Isra’ilawa suka yi shekaru 40 suna cikin salama.

“Mata masu-shelar bisharan kuwa babbar runduna ne.”​—Zabura 68:⁠11