Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 53

Jehoiada Ya Yi Karfin Hali

Jehoiada Ya Yi Karfin Hali

Jezebel tana da ’ya mai suna Athaliah, kuma ita ma muguwa ce kamar mamarta. Athaliah ta auri sarkin Yahuda. Bayan da maigidanta ya mutu, sai yaronta ya zama sarki. Amma da yaronta ya mutu, sai Athaliah ta soma mulkin Yahuda da kanta. Kuma ta yi ƙoƙari ta kashe dukan waɗanda za su zama sarki, har da jikokinta. Hakan ya sa mutane suna jin tsoron ta sosai.

Wani Babban Firist mai suna Jehoiada da matarsa Jehosheba sun san cewa abin da Athaliah take yi ba shi da kyau. Sai suka sa ransu cikin hassada don su ɓoye ɗaya daga cikin jikan Athaliah mai suna Jehoash. Kuma suka kula da shi a cikin haikalin.

Sa’ad da Jehoash ya kai shekara bakwai, sai Jehoiada ya kira dattawa da Lawiyawa kuma ya ce masu: ‘Ku tsare ƙofofin haikalin kuma kada ku bar kowa ya shiga.’ Sai Jehoiada ya naɗa Jehoash sarkin Yahuda kuma ya saka masa rawani a kai. Mutanen Yahuda suka yi ihu suka ce: ‘Ran sarki shi daɗe!’

Sarauniya Athaliah ta ji ihun da mutanen suke yi, sai ta gudu ta je haikalin. Da ta ga sabon sarkin, sai ta yi ihu ta ce: “Kai, Cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!” Sai dattawan suka kama muguwar sarauniyar kuma suka kashe ta. Amma abubuwa marasa kyau da ta sa mutanen su riƙa yi fa?

Jehoiada ya taimaka wa mutanen su yi wa Jehobah alkawari cewa za su bauta masa shi kaɗai. Jehoiada ya sa suka rushe haikalin Baal kuma suka farfashe gumaka. Ya naɗa firistoci da kuma Lawiyawa a haikalin don mutane su soma bauta wa Jehobah a wurin. Ya saka masu gadi  a haikalin don kada su bar wani marar tsarki ya shigo ciki. Bayan haka, sai Jehoiada da kuma dattawan suka kai Jehoash cikin fāda kuma suka ajiye shi a kan kursiyinsa. Yahudawa sun yi farin ciki sosai. Yanzu sun sami ’yancin bauta wa Jehobah, sun daina bauta wa Baal kuma sun daina jin tsoron Athaliah. Ka ga yadda ƙarfin halin da Jehoiada yake da shi ya taimaka wa mutane da yawa?

“Kada ku ji tsoron waɗannan da suke kisan jiki, ba su kuwa da iko su kashe rai: gwamma dai ku ji tsoron wannan wanda yana da iko ya hallaka rai duk da jiki.”​—Matta 10:28