Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 24

Ba Su Cika Alkawarinsu Ba

Ba Su Cika Alkawarinsu Ba

Jehobah ya ce wa Musa: ‘Ka zo ka same ni a kan dutse. Zan ba ka dokokina a kan allon dutse.’ Sai Musa ya hau kan dutsen kuma ya yi kwana 40 a wurin dare da rana. Yayin da yake wurin, Jehobah ya rubuta Dokoki Goma a kan allunan dutse guda biyu. Sai ya ba Musa allunan.

Bayan wani lokaci, sai Isra’ilawan suka soma tunanin cewa Musa ba zai dawo ba. Sai suka ce wa Haruna: ‘Muna son wani da zai ja-gorance mu. Ka ƙera mana allah!’ Haruna ya ce: ‘Ku ba ni gwal.’ Sai ya yi amfani da ita wajen ƙera musu ƙaramin sā na gwal. Mutanen suka ce: ‘Wannan ƙaramin sān ne Allahn da ya fito da mu daga ƙasar Masar.’ Suka soma bauta masa kuma suka yi babban biki. Shin yin hakan ya dace? A’a, domin mutanen sun yi alkawari cewa za su bauta wa Jehobah kaɗai. Amma yanzu, ba su cika alkawarinsu ba.

Jehobah yana ganin abin da yake faruwa sai ya gaya wa Musa cewa: ‘Ka koma wurin mutanen. Sun ƙi bin  umurnina kuma suna bauta wa allahn ƙarya.’ Sai Musa ya sauko daga dutsen, yana riƙe da alluna biyu.

Da Musa ya zo kusa da wurin da mutanen suke, sai ya ji suna waƙa. Sai ya ga suna rawa kuma suna bauta wa ƙaramin sān. Musa ya yi fushi sosai. Sai ya jefar da alluna biyun a ƙasa kuma suka farfashe. Nan da nan sai ya yi kaca-kaca da gunkin. Sai ya tambayi Haruna: ‘Me ya sa ka saurari mutanen nan kuma ka yi musu gunki?’ Sai Haruna ya ce: ‘Kada ka yi fushi. Kai ma ka san halin mutanen nan. Sun ce a yi musu allah kuma da na saka gwal ɗinsu cikin wuta, sai ya zama wannan ƙaramin sā!’ Abin da Haruna ya yi bai dace ba. Sai Musa ya sake hawa dutsen kuma ya roƙi Jehobah ya gafarta wa mutanen.

Jehobah ya gafarta wa Isra’ilawa da suke so su yi masa biyayya. Wannan labarin ya nuna dalilin da ya sa yake da muhimmanci Isra’ilawa su bi ja-gorancin Musa, ko ba haka ba?

‘Sa’ad da kake yin [alkawari] a gaban Allah, ka biya ba tare da jinkiri ba; gama ba ya jin daɗin wawaye: sai ka biya abin da ka yi wa’adinsa.’​—Mai-Wa’azi 5:4