Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARASI NA 17

Musa Ya Bauta wa Jehobah

Musa Ya Bauta wa Jehobah

Sa’ad da Yakubu da iyalinsa suke ƙasar Masar, an soma kiransu Isra’ilawa. Bayan da Yakubu da Yusufu suka mutu, wani Fir’auna ya soma sarauta. Ya ji tsoro cewa Isra’ilawa za su fi mutanen ƙasar Masar yawa. Sai wannan Fir’aunan ya sa Isra’ilawa suka zama bayi. Ya sa su dole su riƙa yin bulo da kuma aiki a gonakinsu. Amma cin zalin da mutanen ƙasar Masar suka yi musu bai hana su yin yawa ba. Da yake Fir’auna ba ya son su yi yawa, sai ya ce a riƙa kashe yara maza da aka haifa. Isra’ilawa sun ji tsoro sosai, ko ba haka ba?

Wata ’yar Isra’ila mai suna Jochebed ta haifi wani jariri mai kyaun gaske. Don kada a kashe shi, sai ta saka shi cikin kwando kuma ta ɓoye shi a ciyayin da ke bakin Kogin Nilu. Sai ’yar’uwar jaririn mai suna Maryamu ta tsaya a wurin don ta ga abin da zai faru da shi.

Da ’yar Fir’auna ta zo wanka a kogin, sai ta ga kwandon. Ta ga jariri a ciki yana kuka kuma  ta ji tausayinsa. Sai Maryamu ta ce: ‘In nemo miki matar da za ta kula da shi?’ Sa’ad da ’yar Fir’auna ta yarda, sai Maryamu ta je ta kawo mahaifiyar jaririn, wato Jochebed. Sai ’yar Fir’auna ta ce: ‘Ki ɗauki wannan yaron, ki yi mini renonsa, zan ba ki kuɗi.’

Da yaron ya girma, Jochebed ta kai shi wurin ’yar Fir’auna. Sai ’yar Fir’auna ta saka masa suna Musa kuma ya zama ɗanta. Musa ya zama yarima kuma zai iya samun duk abin da yake so. Amma bai manta da Jehobah ba. Ya san cewa asali shi ɗan ƙasar Isra’ila ne ba Masar ba. Saboda haka, ya yanke shawarar bauta wa Jehobah.

A lokacin da Musa ya kai shekara 40, sai ya ce yana son ya taimaka wa mutanensa. Da ya ga wani ɗan Masar yana wahalar da wani ɗan Isra’ila, sai ya kashe ɗan Masar ɗin. A lokacin da Fir’auna ya ji labarin, sai ya so ya kashe Musa. Amma Musa ya gudu zuwa ƙasar Midiya. Kuma Jehobah ya kula da shi a wurin.

‘Ta wurin bangaskiya Musa . . . ya ƙi yarda a ce da shi ɗan ’yar Fir’auna; ya fi so a wulaƙanta shi tare da mutanen Allah.’​—Ibraniyawa 11:​24, 25